Abba Kabir Ya Fadawa 'Yan Arewa Muhimmancin Goyon Bayan Tinubu
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana goyon bayansa ga ci gaba da tsarin sauya kujerar Shugaban Ƙasa tsakanin Arewa da Kudancin Najeriya
- Gwamnan ya ce ya kamata kowane ɓangare ya samu damar riƙe mulkin ƙasa na wa’adin shekara takwas kafin a miƙa shi ga ɗayan ɓangaren
- Ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da su mayar da hankali kan manufofi da shirye-shiryen ci gaba maimakon hare-haren siyasa da kalaman da za su iya kawo rikici
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira da a ci gaba da tsarin sauya kujerar Shugaban Ƙasa tsakanin Arewa da Kudancin Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a fadar gwamnatin Kano, yayin da yake ƙaddamar da motoci 50 da Oweizide Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya bayar domin tallafa wa gangamin APC a Kano gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
"Ka ba mutane hakuri," Atiku ya sake tono abin da Bola Tinubu ya aikata a Najeriya

Source: Twitter
Dalilin goyon bayan Tinubu
Sanusi Bature ya wallafa a Facebook cewa Abba Kabir Yusuf ya ce matsayarsa ta samo asali ne daga ra’ayin cewa ya kamata ikon Shugaban Ƙasa ya riƙa sauyawa tsakanin Arewa da Kudu.
Ya ce kowane ɓangare ya kamata ya samu damar samar da Shugaban Ƙasa na wa’adin mulki biyu a jere, domin ba wa gwamnati isasshen lokaci ta aiwatar da manyan manufofi, shirye-shirye da ayyukan raya ƙasa.
Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan siyasa, musamman a Arewa, da su yi haƙuri domin tsarin da ake ciki ya kammala wa’adinsa.
Abba ya yi magana kan 2027
Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan Kano ya yi kira da a goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu.
A cewar gwamnan, hakan zai ba Kudancin Najeriya damar kammala zagayen wa’adin mulki biyu kafin a sake mayar da mulkin Shugaban Ƙasa zuwa Arewa a shekarar 2031.

Kara karanta wannan
Gwamna ya hango abin da ba zai wa 'yan Najeriya daɗi ba kan dawo da tallafin fetur

Source: Facebook
Ya ce tsarin sauya mulki tsakanin Arewa da Kudu na iya taimakawa wajen inganta adalci, haɗin kan ƙasa, amincewa da juna da kuma bai wa ’yan Najeriya daga sassa daban-daban damar jin cewa suna da matsayi a cikin ƙasa.
Abba ya buƙaci kamfen cikin lumana
Gwamnan ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa da su gudanar da kamfen cikin lumana tare da mayar da hankali kan batutuwa masu muhimmanci gabanin zaɓen 2027.
Ya buƙaci ’yan siyasa su fi mayar da hankali kan manufofi, shirye-shirye da tsare-tsaren ci gaba, maimakon kai wa juna hare-hare ko amfani da kalaman da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya.
Abba ya sake jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa harkokin siyasa da dimokuraɗiyya cikin lumana, tare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su fifita haɗin kan Kano da Najeriya a kan bambance-bambancen siyasa.
APC ta yi magana kan Wike
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu shugabannin APC na jihohi sun yi watsi da ƙungiyar Rainbow Coalition da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta.
Shugabannin jam’iyyar sun bukaci Wike ya koma APC a hukumance idan da gaske yake son taimaka wa Shugaba Bola Tinubu wajen sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sai dai wasu sassan APC sun ce za su marabci Wike idan ya koma jam’iyyar, yayin da wasu suka ce ba za su amince da tsarin da zai raba goyon bayan ’yan takara a matakan daban-daban na zaɓe ba.
Asali: Legit.ng
