Gwamnati Za Ta Samar Wa Matasan Najeriya Ayyuka a Kasashen Waje, An Ji Yadda Tsarin Yake

Gwamnati Za Ta Samar Wa Matasan Najeriya Ayyuka a Kasashen Waje, An Ji Yadda Tsarin Yake

  • Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin samar da ayyukan yi miliyan daya da ke da alaƙa da fitar da kayayyaki zuwa ketare nan da shekarar 2030
  • Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ce kasuwar kayan da ake fitarwa zuwa wasu ƙasashe na duniya za ta haura $1trn a shekaru masu zuwa
  • Ya ce Najeriya na da damar cin gajiyar wannan kasuwa saboda yawan matasa masu ƙwarewar fasahar zamani da iya Turanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta shirya samar da ayyukan yi miliyan ɗaya da ke da alaƙa da fitar da kayayyaki da ayyuka zuwa ketare nan da shekarar 2030.

Gwamnatin ta dauki aniyar haka ne yayin da Najeriya ke neman samun kaso mafi girma daga kasuwar ayyukan kasashen waje da ke ci gaba da bunƙasa a duniya.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta nema a taron UNGA karo na 81

Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Daily Trust ta ce Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar da shirin Hire From Nigeria (dauki ma'aikata daga Najeriya) da aka gudanar a New York, a gefen Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya.

Najeriya za ta samar wa matasa ayyuka

Jawabin Shettima, wanda Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, ya gabatar, ya ce ana sa ran kasuwar kayan da ake fitarwa zuwa wasu ƙasashe za ta haura dala tiriliyan ɗaya a shekaru masu zuwa.

Ya ce Najeriya, wadda ke da dimbin matasa masu ƙwarewar fasahar zamani da kuma iya Turanci, na da kyakkyawar damar cin gajiyar karuwar buƙatar ƙwararrun ma’aikata a duniya.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana shirin a matsayin “ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da ake samun damar inganta tattalin arziki a tarihin zamani”, yana mai kokawa kan yadda aka bar Afirka a baya a wannan kasuwa.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya fadi wanda zai iya nasara a 2027, ya cire Tinubu a lissafi

“Saboda haka, ina bayyana muku a fili cewa: Najeriya ce sabuwar cibiyar da kasuwar ayyukan yi ta duniya za ta karkata gare ta,” in ji shi.

Gwamnatin Tinubu ta hada kai da kamfanoni

Ministar Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Jumoke Oduwole, ta ce shirin ya yi daidai da abubuwan da gwamnati ta sa a gaba kan matasa, samar da ayyukan yi, da bunkasa harkokin kasuwancin zamani.

Ta ce gwamnati na aiki tare da kamfanoni masu zaman kansu domin sauya tsarin samar da ƙwararrun ma’aikata a ƙasar da kuma cin gajiyar damar da ke akwai a kasuwar ayyukan yi ta duniya.

Jami'an gwamnati.
Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa tare da wasu manyan jami'an gwamnatin tarayya a wurin kaddamar da shirin Hire From Nigeria a birnin New York Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Twitter

Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya ce Najeriya ta yi asarar damar shiga wannan kasuwa tun shekaru 25 zuwa 30 da suka gabata, amma ya ce gwamnati ta ƙuduri aniyar kada ta sake maimaita hakan.

Ya ce sauye-sauyen da ake yi a fannin ilimi na da nufin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun samu ƙwarewar da za ta ba su damar samar da mafita tare da samun kuɗin shiga.

Ana shirin samar da ayyuka a fannin fasaha

Kara karanta wannan

Abubuwan da Shettima ya fada kan Najeriya a taron majalisar dinkin duniya

Kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na samar da ayyukan yi ga mutne miliyan biyu a fannin fasaha zuwa shekarar 2030.

Gwamnatin ta ce tana ci gaba da kokarin ƙoƙarin mayar da al’adun ƙasar da baiwar masu fasaha zuwa harkokin kasuwanci masu samar da kuɗaɗen shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262