Gwamna Ya Raba Gardama kan Surutun da Ake Yi game da Mulkin Peter Obi a Anambra
- Alex Otti ya ce Peter Obi ya bar dala miliyan 155 a asusun Anambra da ya tashi barin mulki a shekarar 2014
- Otti ya ce ya shawarci Obi ya canza kudin daga naira zuwa dala saboda faduwar darajar kudin Najeriya
- Idan har an bar kudin a banki zuwa 2019, darajarsu za ta karu daga Naira biliyan 25 zuwa Naira biliyan 95
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abia - Alex Otti wanda yanzu shi ne gwamnan jihar Abia, ya zama lauyan Peter Obi wanda aka hasko lokacin mulkinsa.
Gwamna Alex Obi ya shaida wa duniya cewa Peter Obi ya adana wa jihar Anambra $155m a banki a sa’ilin da yake ofis.

Source: Facebook
Peter Obi ya adana wa jihar Anambra $155m
Mai girma gwamnan ya tabbatar da wannan zance ne a lokacin da tashar Arise ta yi wata doguwar hira da shi a makon jiya.

Kara karanta wannan
Abin da ya shuka a mulki ne yake girba, Sanata Shehu Sani ya jero zunuban El Rufai
Alex Otti shi ne shugaban bankin Diamond a Najeriya lokacin da gwamnatin Peter Obi ta ajiye wadannan makudan kudi.
Daga baya bankin Diamond ya hade da Access, shi kuma Otti ya shiga harkokin siyasa.
Yadda aka canza kudin zuwa daloli a banki
Mista Otti ya ce da farko Obi ya yi niyyar ajiye kudin ne a Naira, amma sai shi ya ba shi shawarar ya canza su zuwa dala.
Haka Obi wanda yanzu yake neman takarar shugaban kasar ya maida wadannan biliyoyin kudi zuwa dalolin Amurka.
Kamar yadda ya bayyana, hikimar yin hakan ita ce ko da Naira ta karye, kudin mutanen Anambra ba za su rasa daraja ba.
Wannan bayanin yana da muhimmanci ganin yadda gwamnatin Charles Soludo ta taso Obi a gaban shekaru da barin ofis.
Rigimar Peter da gwamnatin jihar Anambra
Sahara Reporters ta rahoto ‘dan takaran na NDC a babban zaben 2027 yana dage wa cewa lallai ya bar kudi a baitul-mali.
Gwamnatin Anambra ta yanzu kuwa ta ce Obi ya bar bashin $1237m na kudin da ya karbo aro daga wasu bankunan kasar waje.
Ko ma ya karbo aron wadannan kudi, tsohon gwamnan ya ce ai ya bar dukiyar da za ta isa a biya bashin har a samu wasu canji.
Gwamna Otti ya jinjina wa aikin Obi
Otti ya ce ya taba yin rubutu a jaridar This Day tun 2020, inda ya yaba da irin tsantseni da gaskiyar Peter Obi wajen kashe kudi.
Duk da ba su jam’iyya guda a lokacin, gwamnan na Abia ya jinjina wa tsohon gwamnan wanda suka yi zama a jam'iyyar LP tare.
Lokacin da Obi ya adana dalolin, darajarsu ba ta wuce N25bn, amma sai da ta kai za su wuce N95bn saboda ruwa da ya karu.

Source: Facebook
Dangote yana hangen kusan N50tr a shekara
Rahoton nan cewa yake yi Aliko Dangote ya jaddada cewa manufarsu ita ce tabbatar da cewa suna cin riba ta sama da $30bn a shekara.
Ana so kimar rukunin kamfanonin ta kai akalla dala biliyan 350 a kasuwa idan aka fito da hannun jari nan da shekaru hudu masu zuwa.
Mai kudin nahiyar Afrika zai gina matata da masana’antar NLG a kasar Kenya wadanda za su ci $8bn kamar yadda aka bayyana.
Asali: Legit.ng
