Siyasar 2027: Abba Kabir Yusuf zai Karfafi 'Yan Kannywood
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyarsa ta tallafa wa Kannywood domin bunƙasa matasa da tattalin arzikin jihar
- Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da yanayin da zai ba mawaƙa, ‘yan fim da sauran masu fasaha damar amfani da basirarsu
- Abba Yusuf ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi shugabanni da mambobin Tripple R masu goyon bayan shugaba Bola Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta tallafa wa Kannywood da sauran masu ruwa da tsaki domin bunƙasa jihar.
Gwamnan ya ce tallafin zai taimaka wajen inganta shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ajandar Kano First da gwamnatinsa ke aiwatarwa.

Source: Facebook
Sanarwar da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a Facebook ta bayyana cewa Abba ya yi wannan magana ne yayin da ya karɓi 'yan Kannywood.
Alakar Abba da 'yan Kannywood
Gwamna Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa mawaƙa, masu shirya fina-finai, ‘yan wasa da sauran masu fasaha ta hanyar samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar bunƙasa baiwarsu.
Ya ce hakan zai taimaka masu wajen dogaro da kai da kuma bayar da gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arzikin Kano.
Ya kuma tabbatar wa masu ruwa da tsaki a Kannywood cewa gwamnatinsa za ta ƙarfafa haɗin gwiwa da masana’antar tare da tallafa wa shirye-shiryen da za su samar da damammaki masu ɗorewa ga masu fasaha.
Gwamnan ya buƙaci masu ruwa da tsaki a masana’antar da su yi amfani da kafafen da suke da su wajen yaɗa zaman lafiya, haɗin kai, ci gaba.

Source: Facebook
APC ta yi hasashen nasara
Shi ma shugaban APC na Kano, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar za ta samu gagarumar nasara a babban zaɓen 2027.
Doguwa ya ce APC ta himmatu wajen ganin an gudanar da zaɓe cikin zaman lafiya, gaskiya da sahihanci, yana mai fatan jam’iyyar za ta yi nasara a dukkan matakai.
Ya buƙaci ‘yan jam’iyyar da magoya bayanta su kasance cikin haɗin kai tare da mayar da hankali wajen bunkasa nasarorin da gwamnatin APC ta samu a Kano da kuma matakin tarayya.
APC za ta karbi mutane a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa APC a Kano ta shirya karɓar wasu manyan mutane daga jam’iyyun siyasa daban-daban a wani taron da aka shirya gudanarwa a jihar.
Daga cikin waɗanda ake sa ran za su shiga APC akwai Sanata Rufa’i Sani Hanga da mutanensa, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da mutanensa da kuma Sanata Mas’ud Eljibrin Doguwa.
Haka kuma, ana sa ran Hon. Ali Datti Yako da wasu shugabannin NDC, Hon. Badaru Umar da ‘yan tawagar Gawuna, Rt. Hon. Isyaku Ali Danja za su halarci taron.
Asali: Legit.ng

