Ministar Abuja Ta Yi Dogon Hasashen Wanda Tinubu Zai Mika wa Mulki a 2031

Ministar Abuja Ta Yi Dogon Hasashen Wanda Tinubu Zai Mika wa Mulki a 2031

  • Shugaba Bola Tinubu zai yi mulki na tsawon shekaru takwas har zuwa karshen Mayun shekara ta 2031
  • Mariya Mahmud tana fatan jam'iyyar APC ce za ta sake lashe zabe kuma ta mika wa dan jam’iyyarta mulki
  • Karamar ministar ta Abuja tana da kwarin gwiwar cewa al'umma za su ci gaba da goyon bayan manufofinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Karamar ministar harkokin Abuja, Mariya Mahmud ta ba jam’iyyarsu ta APC nasara har bayan zabe mai zuwa nan da watanni.

Mariya Mahmud ta na ganin Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben shugaban kasa kuma har APC ta kuma yin nasara a shekarar 2031.

Bola Tinubu
Bola Tinubu lokacin da ya kama rantsuwar mulki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wa zai gaji shugaba Bola Tinubu a 2031?

Ministar ta yi wannan magana ne wajen taron kungiyar City Boy Movement (CBM) a Kano kamar yadda Daily Trust ta fada.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027

Mariya Mahmud ta tabbatar wa ‘yan kungiyar ta magoya bayan Bola Tinubu cewa fadar Aso Rock ba za ta yi ango a badi ba.

‘Yar siyasar ta ke cewa babu wani mutum dabam da zai shiga cikin Aso Villa sai a 2031.

Idan APC ta lashe babban zabe, tana fatan za ta sake maimaita wannan a 2031 don mulki ya cigaba da zama cikin jam’iyyar tasu.

Mariya ta yi farin ciki da tafiyar City Movement

Karamar ministar ta yabi wannan tafiya, ta ke cewa ta zama hanyar jawo matasa da mata su iya tallata tazarcen Bola Tinubu.

Baya ga taya Tinubu yakin neman zabe, ministar ta ce ‘yan City Boy Movement za su taimaka wajen tabbatar da galabar APC.

Najeriya tana matasa da sun kai 60-70% na adadin al’ummar kasar, don haka Mariya Mahmud ta ke farin ciki da wannan tafiya.

Ta ce duk abin da aka yi ba tare da an jawo matasa ba, ba zai yi nasara a kasar nan.

Kara karanta wannan

Sarakuna sun bi bayan ‘dan takaran APC a zaben gwamna, an san makomar Tinubu a Yobe

Baya ga matasa, ta ji dadin yadda ta ga mata a cikin kungiyar City Boy Movement kamar yadda labarin ya zo har a The Eagle.

Abubuwan da za su sa a zabi Tinubu

A jawabin da ta yi ranar Litinin, ta yi kokarin ambato nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a shekaru uku da watannin da ta yi.

Mai girma ministar ta bada misali da tsarin NELFund da aka fito da shi domin ganin babu ‘dan talakan da ya gaza cigana da karatu.

A zaben shugaban kasa da za a yi, ministar ta ce ayyukan a-yaba da shugaba Tinubu ya yi shi za su tallata shi a jihohin Najeriya.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da 'yan APC lokacin da ya samu tutar 2027 Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Masoyan Tinubu suna neman mutum miliyan 10

An yi wannan ne lokacin da CBM ta sha alwashin ganin ‘yan kungiyar sun kai miliyan 10 domin su samu ta-cewa a fagen siyasa.

Darekta Janar na CMB, Francis Oluwatosin Shoga ya ce idan suka samu wannan adadi, sai yadda suka yi idan aka shiga zabe.

Shugaban kungiyar a Kano, Nasir Bala Ja’oji ya ce zuwa yanzu sun yi wa mutane fiye da 189, 000 rajista a matsayin ‘yan tafiyarsu.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta fallasa shirin da aka yi wajen tarbar dumbin mutane zuwa APC a Kano

‘Sai Tinubu da Wali’ in ji Sarakunan Yobe

Sarakunan gargajiya sun goyi bayan ‘yan takaran APC a Yobe a zaben shugaban kasa da na gwamna kamar yadda rahoto ya gabata.

Sarakunan Yobe sun goyi bayan takarar gwamna ta Baba Malam Wali da tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a takarar da za a yi a 2027.

'Dan takaran gwamnan ya yi wannan bayani bayan ya gama ziyara zuwa fadar sarakunan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng