Bill Gates Yana Tsoron Fasahar AI Za Ta Iya Kashe Mutum Biliyan 1 a Duniya

Bill Gates Yana Tsoron Fasahar AI Za Ta Iya Kashe Mutum Biliyan 1 a Duniya

  • Bill Gates ya yi gargadi mai tsanani kan AI, yana cewa fasahar na da ƙarfin da za ta iya jawo mutuwar mutane biliyan daya
  • Tsohon shugaban Microsoft ya bukaci gwamnati ta tsaurara dokokin da za su hana amfani da ita wajen haddasa barna
  • Gates ya ce barin AI ba tare da isasshen sa ido ba abu ne mai matuƙar hafari, domin masu mugun nufi na iya kawo matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

America - Tsohon babban mai kudi a duniya, Bill Gates ya yi mummunan gargadi game da amfani da fasahar AI haka kurum babu kaidi.

Bill Gates ya ce idan aka cigaba da tafiya ba tare da sa-ido ba, kirkirarriyar basirar za ta iya jawo mutuwar mutane har biliyan daya.

Bill Gates
Dandazon jama'a a kasar Slovakia da kuma Mista Bill Gates yana magana Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bill Gates yana ganin barazana tattare da A.I

A wata hira da tashar NBC, Bill Gates ya ce samun bata-gari da fasahar AI barazana ce ga wanzuwar bil Adama a kan doron kasa.

Kara karanta wannan

Abin da ya shuka a mulki ne yake girba, Sanata Shehu Sani ya jero zunuban El Rufai

Attajirin yana tsoron za a iya amfani da AI wajen kirkirar makami ko wata cuta ta hallaka jama'a.

Bill Gates ya ce zai yi wahala fasahar ta AI ta iya bambance masu amfana da ita wajen yin bincike na kwarai da ja'irai masu sharri a duniya.

Akwai wadanda suke amfani da AI a yau wajen ayyukan da za su taimaki al’umma kamar kere magunguna da nufin a samu lafiya.

Haka kuma ana gudun a iya ta’addanci da kwayoyin halitta ta hanyar kirkiro halittu masu kawo cututtuka.

Bukatar a sa ido a kan karfin A.I

Ya yi gargadin ne a lokacin da kasashen duniya suke kara jan kunne game da karfin AI, suna kira da cewa a dage wajen sa wa fasahar ido.

The Guardian ta rahoto Gates yana fada wa Kristen Welker bukatar ‘yan siyasa su duba yadda za a ba jama’a kariya daga barnar AI.

Kara karanta wannan

Barayin waya sun shiga gida sun kashe uwa mai yara 5 da wuka a Gombe

Tsohon shugaban na Microsoft yake cewa hakan ya zama dole saboda karfin fasahar a yau.

A tattaunawar ne aka ji yana fada wa ‘yar jaridar mai shekara 50 cewa A.I yana da karfin da zai yi sanadiyyar mutuwar mutane rututu.

Ya ce bil Adama biliyan daya za su iya sheka wa barzahu a sanadiyyar tasirin aikin fasahar.

"Ba a taba samun makami mai karfi irin tarayyar mutane masu muguwar manufa da kuma sababbin fasahar AI ba."

- Bill Gates

Mr. Bill Gates
Tsohon mai kudi a duniya, Mr. Bill Gates yana wani jawabi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bill Gates yana amfani da A.I?

Mista Gates ya yi magana game da batun da ake yi na cewa za a samar da fasahar rufe AI idan har aka ga karfinsa ya yi yawa.

Babban attajirin yana ganin yin hakan bai isa ya magance matsalar da za a iya fuskanta ba.

Shi a karon kan shi ya amsa cewa yana amfani da kirkirarriyar basirar, amma ya ce aiki yake yi da ba shi ba harkokin wasa ba.

Wasiyyar da Bill Gates ya bari

Ana da labari cewa Bill Gates wanda hamashin mai kudi ne ya sanar da aniyarsa ta kyautar da gaba ɗaya dukiyarsa a cikin shekaru 20 masu zuwa.

Kara karanta wannan

"Allah ne ya cece ni," Gwamna ya ba da labarin yadda aka yi yunkurin kashe shi a gidansa

Ya bayyana wannan mataki a matsayin 'babi na ƙarshe na rayuwarsa', inda ya yanke shawarar sadaukar da tulin dukiyar domin ceton al'umma.

Attajirin, wanda mujallar Forbes ta ƙiyasta dukiyarsa ta haura $100bn, ya ce gidauniyarsa ta Bill & Melinda Gates Foundation za ta daina aiki a 2045.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng