Babbar Magana: NNPP Ta Gano Wanda Zai Ci Amana tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

Babbar Magana: NNPP Ta Gano Wanda Zai Ci Amana tsakanin Kwankwaso da Peter Obi

  • NNPP ta gargadi NDC da Peter Obi kan zaɓen Rabiu Kwankwaso a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027
  • Sakataren NNPP, Ogini Olaposi, ya kira zaɓen Kwankwaso “babban kuskure”, yana mai zargin tsohon ɗan takarar jam’iyyar zai ci amanar NDC
  • NNPP ta ce tarihin siyasar Kwankwaso da rikicinsa da jam’iyyar bayan zaɓen 2023 ya kamata ya zama darasi ga NDC kafin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar NNPP ta gargadi NDC da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, kan zaɓen Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

An gano manyan abubuwa 2 da za su yi tasiri a zaben 2027

NNPP ta yi zargin cewa Kwankwaso, wanda ya yi wa jam’iyyar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, na iya daga baya juya wa NDC baya.

Kwankwaso zai yi takara tare da Peter Obi
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Sakataren NNPP, Ogini Olaposi, ya bayyana matsayar jam’iyyar a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 7 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar Vanguard.

NNPP ta kira zaɓen Kwankwaso kuskure

Jam’iyyar ta ce bambance-bambancen siyasar da suka samu tsakaninta da Kwankwaso bayan zaɓen 2023 ya kamata ya zama babban darasi ga NDC.

Olaposi ya bayyana zaɓen Kwankwaso a matsayin mataimakin Peter Obi da cewa “babban kuskure ne”, yana mai cewa NDC ya kamata ta binciki tarihin siyasar Kwankwaso kafin ta yanke wannan hukunci.

“Shi ya sa ya kamata jam’iyyun siyasa su yi taka-tsantsan wajen zaɓen waɗanda za su zama mataimakan ’yan takara da masu riƙe tutar jam’iyya,” in ji shi.

Ya zargi Kwankwaso da juya wa NNPP baya duk da damar da jam’iyyar ta ba shi na yin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin tutarta a 2023.

Kara karanta wannan

Pantami na shirin fafatawa a 2027, PDP ta gamu da cikas a Gombe

An zargi Kwankwaso da cin amanar NNPP

Olaposi ya ce NNPP ta ba Kwankwaso wata dama da ba kasafai ake samu ba, ciki har da ba shi tikitin takara ba tare da hamayya ba.

A cewarsa, wannan damar ce ta taimaka wajen mayar da Kwankwaso cikin manyan ’yan siyasar da ake tattaunawa da su kan shugabancin Najeriya a halin yanzu.

“Wannan dama ta musamman da NNPP ta ba Kwankwaso a 2023, baya ga tikitin da aka ba shi kyauta, ita ce ta kawo shi sahun gaba na tattaunawar shugabancin ƙasa a Najeriya a yanzu,” in ji shi.

Ya kuma yi zargin cewa matakan Kwankwaso sun taimaka wajen haifar da rikicin cikin gida a NNPP, wanda ya kai ga ficewar wasu mambobin jam’iyyar.

“Ba za mu manta cikin gaggawa yadda ya lalata jam’iyyar ba, lamarin da ya sa mambobinmu suka fice da yawa. Zai ci amanar NDC haka nan, nan ba da daɗewa ba,” in ji Olaposi.

NNPP ta musanta an miƙa wa Kwankwaso jam’iyyar

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan gudun hijira a Kano ba ta son ganin Ali Modu Sheriff a gangamin yakin neman zaben APC

A wani ɓangare, Olaposi ya musanta ikirarin cewa wanda ya kafa NNPP, Dr Boniface Aniebonam, ya miƙa jam’iyyar ga Kwankwaso.

Ya bayyana wannan ikirari a matsayin abin da ba za a iya tunaninsa ba, yana mai cewa ba za a iya cewa an miƙa ikon jam’iyyar ba tare da an miƙa takardar rajistar jam’iyyar ta asali ba.

Kwankwaso zai yi wa Peter Obi mataimaki
Peter Obi tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a wajen taron NDC Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya yi magana kan makomar Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi magana kan makomar Najeriya.

Sanata Kwankwaso ya bayyana kyakkyawan fata cewa Najeriya za ta shawo kan ƙalubalen da take fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng