Zaɓen 2027 Ta Fara Zafi, Obi da Kwankwaso Sun Tura Ƙalubale ga Ƴan Najeriya

Zaɓen 2027 Ta Fara Zafi, Obi da Kwankwaso Sun Tura Ƙalubale ga Ƴan Najeriya

  • Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Sanata Rabi'u Kwankwaso sun kalubalanci yan Najeriya
  • Obi ya ce shi da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, sun bayyana bayanansu da tarihin karatunsu domin ’yan Najeriya su bincika su tabbatar da gaskiyar lamarin
  • Tsohon gwamnan Anambra ya kuma ce duk mai neman babban mukamin siyasa ya kamata ya samu nasara ta hanyar ingantaccen tsarin zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya bugi kirji kan tarihinsa da na Rabi'u Kwankwaso.

Peter Obi ya ƙalubalanci ’yan Najeriya da su binciki tarihinsa tare da bayyana duk wani laifi da ya aikata.

Obi da Kwankwaso sun kalubalanci yan Najeriya
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da mataimakin, Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Facebook

Obi ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Port Harcourt, babban birnin Rivers, yayin wani taron tattaunawa da masu zaɓe, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

"Ka yi yadda na yi," Atiku ya sake kinkimo magana mai girma kan bayanan Tinubu na Amurka

Maganganunsa sun zo ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan tarihin rayuwa da bayanan manyan ’yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, ciki har da Atiku Abubakar da Bola Tinubu.

Haka kuma, an mayar da hankali kan tarihin karatun ’yan takarar uku bayan sun cire takardun shaidar makarantun firamare da sakandare daga bayanan kansu da suka miƙa wa INEC a ƙarshen watan Yuli.

Tsohon gwamnan Anambra ya ce shi da abokin takararsa, Rabiu Kwankwaso, sun bayyana tarihin rayuwarsu da bayanansu a fili domin ’yan Najeriya su bincika su tabbatar da gaskiyarsu.

Ya ce:

“Ina so in bai wa kowane ɗan Najeriya damar sanin ko ni wanene.
“Dukkanmu mun gabatar da tarihin rayuwarmu, tun daga ranakun haihuwarmu zuwa makarantun da muka yi, ilimi da sauran bayanai, ga jama’a. Za ku iya bincika ku tabbatar da tarihinmu a ko’ina a duniya.”

Obi ya kuma yi magana a kaikaice kan ƙarar da ya shigar gaban kotu kan Kenneth Okonkwo, wanda ya kasance kakakinsa a yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ya shigar da ƙarar ne bisa zargin cewa Okonkwo, jarumin Nollywood, ya yi kalaman ɓatanci game da harkokinsu da abubuwan da suka faru a baya.

Kara karanta wannan

Okonkwo ya haska dalilin da ya sa ba a son Atiku ya zama shugaban kasa

Tsohon gwamnan ya ce ya ɗauki matakin shari’a ne saboda Okonkwo ya yi iƙirarin cewa yana da wasu bayanai masu tayar da hankali game da tarihinsa.

“Mun kai wani mutum kotu. Ya ce ya san wani abu da zai iya faɗa, wanda zai sa mutane su yi mamaki. Sai na ce masa ina so ka faɗi abin da zai sa mutane su yi mamaki.
“Kuma ina ƙalubalantar kowane ɗan Najeriya. Idan akwai wani abu da kuka sani na aikata wanda ba daidai ba ne, ku fito ku faɗa yanzu.
“Ina ƙalubalantar duniya baki ɗaya: idan kun san wani abu da Rabiu Musa Kwankwaso ya aikata wanda ba daidai ba ne, ku fito ku faɗa yanzu.”

- Peter Obi

A cewar Obi, duk wanda ke neman babban mukamin siyasa ya kamata ya samu damar zuwa wannan matsayi ta hanyar ingantaccen tsari

Obi, Kwankwaso sun gana da Amaechi

An ji cewa dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, da abokin takararsa, Sanata Rabiu Kwankwaso, sun kai ziyartar jaje ga Rotimi Amaechi.

Ziyarar da suka kai Port Harcourt ta biyo bayan rasuwar mahaifiyar Amaechi, inda aka shirya gudanar da jana’izar ta a karshen mako.

Rahotanni sun nuna cewa tsofaffin gwamnoni Obi da Kwankwaso sun mika sakon ta’aziyyarsu ga Amaechi da iyalansa gabanin jana’izar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.