Pantami Na Shirin Fafatawa a 2027, PDP Ta Gamu da Cikas a Gombe

Pantami Na Shirin Fafatawa a 2027, PDP Ta Gamu da Cikas a Gombe

  • Shugaban matasan PDP na Jihar Gombe, Jamilu Ali Kalshingi, ya yi murabus daga mukaminsa da kuma kasancewarsa ɗan jam’iyyar
  • Kalshingi ya ce ya ɗauki matakin ne bayan yin dogon tunani, kuma murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take
  • Murabus ɗin ya zo ne jim kaɗan bayan tsohon ma’ajin PDP na ƙasa, Ahmed Yayari, ya sauya sheƙa zuwa sansanin ɗan takarar gwamnan APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Shugaban matasan babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Gombe, Jamilu Ali Kalshingi, ya yi murabus daga mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar.

An bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙar murabus mai kwanan wata 31 ga Agusta, 2026, wadda Kalshingi ya aika wa shugaban PDP na mazabar Bolari ta Yamma da ke ƙaramar hukumar Gombe.

Kara karanta wannan

Tsakanin Atiku da Obi waye zai iya ƙalubalantar Tinubu? an fadi wanda ya zo da gaske

Shugaban matasan PDP a Gombe ya bar jam'iyyar
Taswirar jihar Gombe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kalshingi ya ajiye mukaminsa

Legit Hausa ta samu kwafin wasiƙar a shafinsa na Facebook, ranar Asabar, 5 ga watan Satumban 2026 inda tsohon shugaban matasan ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne “bayan yin la’akari sosai” da lamarin.

Kalshingi ya ce murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take, ba tare da bayyana wani ƙarin bayani kan dalilin da ya sa ya yanke wannan shawarar ba.

Ya gode wa ’yan jam’iyyar PDP

A cikin wasiƙar, Kalshingi ya bayyana wa’adin da ya yi a matsayin shugaban matasan PDP na jihar a matsayin babban abin alfahari da daraja a gare shi.

Ya kuma gode wa sauran ’yan jam’iyyar da suka yi aiki tare da shi wajen cimma manufofin da suka shafi matasan Jihar Gombe.

“Yin aiki a matsayin shugaban matasan jihar ya kasance babban abin girmamawa, kuma ina godiya da damar da na samu ta yin aiki tare da ’yan jam’iyya masu ƙwazo wajen cimma manufofinmu na matasan Gombe."

Kara karanta wannan

Dan sanda ya yi murabus a Bauchi, ya ce shekaru 2 bai samu albashinsa ba

“Ina alfahari da nasarorin da muka samu,” in ji shi.

Bai bayyana inda zai koma ba

Sai dai tsohon shugaban matasan PDP ɗin ya bayyana cewa yana ɗaukar wata sabuwar hanya a siyasarsa, wadda ta tilasta masa barin jam’iyyar.

Kalshingi bai bayyana jam’iyyar ko sansanin siyasar da zai koma ba, lamarin da ya bar makomar siyasarsa a buɗe.

Ya kuma tabbatar wa magoya bayansa cewa duk da ficewarsa daga PDP, zai ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa ci gaban Jihar Gombe.

Murabus ɗin ya biyo bayan sauya sheƙa

Matakin Kalshingi ya zo ne jim kaɗan bayan tsohon ma’ajin PDP na ƙasa, Ahmed Yayari, ya fice daga jam’iyyar.

Yayari ya sauya sheƙa zuwa sansanin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar APC a Gombe, Dr Jamilu Isiyaku Gwamna.

Sauya sheƙar Yayari da kuma murabus ɗin Kalshingi na zuwa ne yayin da ake ƙara samun sauye-sauyen siyasa a Gombe gabanin zaɓukan 2027.

Kalshingi ya rabu da PDP
Jamilu Ali Kalshingi, tsohon shugaban matasan PDP a Gombe Hoto: Jamilu Ali Kalshingi
Source: Facebook

Pantami ya ci zaben yanar gizo

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar jam'iyyar PDP a Gombe, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya fara nuna rinjaye a fagen siyasar jihar a shirin zaben 2027.

Farfesa Pantami ya ragargaji sauran 'yan takara a zabukan gwaji biyu daban-daban da aka gudanar a tsakanin masu amfani da kafofin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng