Jigo a APC Ya Watsawa Gwamna Kasa a Ido, Ya Ki Karbar Mukamin da Ya Ba Shi

Jigo a APC Ya Watsawa Gwamna Kasa a Ido, Ya Ki Karbar Mukamin da Ya Ba Shi

  • Jigon APC a Okitipupa, Falana Oyewole, ya ƙi karɓar muƙamin mai taimakawa na musamman da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ba shi
  • Oyewole ya ce ya yanke shawarar ne saboda abin da ya bayyana a matsayin wariyar da ake yi wa al’ummar Erinje wajen rabon muƙaman siyasa
  • Ya buƙaci gwamnan ya sake duba rabon muƙaman siyasa tare da bai wa ɗan asalin Erinje muƙami mafi girma da muhimmanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Akure, Ondo - Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a ƙaramar hukumar Okitipupa ta Jihar Ondo, Falana Oyewole, ya ƙi karɓar muƙamin mai taimaka wa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na musamman.

Oyewole ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda damuwarsa kan abin da ya bayyana a matsayin ware al’ummar Erinje wajen rabon muƙaman siyasa a gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue ya tsokano fada, Kwankwaso ya yi masa raddi mai zafi

Jigon APC ya ki karbar mukami daga wajen gwamnan Ondo
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo Hoto: Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Source: Twitter

Oyewole ya rubuta wa gwamnan wasiƙa

Jaridar Daily Trust ta ce Oyewole ya bayyana matsayarsa a wata wasiƙa mai ɗauke da ranar 22 ga Satumba, 2026, wadda ya aika wa gwamnan ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Ondo.

A cikin wasiƙar, ya gode wa Gwamna Aiyedatiwa bisa ganin ya cancanci naɗa shi a matsayin mai taimaka masa na musamman.

Sai dai ya ce bayan tattaunawa mai zurfi da iyalansa da kuma shugabannin siyasa a Ode-Erinje, ya yanke shawarar ba zai karɓi muƙamin ba.

‘An yi watsi da Erinje’

Jigon na APC ya ce abin da ya sa ya ƙi muƙamin shi ne yadda yake ganin an yi watsi da Erinje wajen raba muƙaman siyasa masu muhimmanci a gwamnatin yanzu.

Ya ce al’ummar Erinje na jin “an yi watsi da su matuƙa”, saboda tun bayan kafa gwamnatin Aiyedatiwa ba a bai wa ɗan yankin wani muƙami na siyasa mai muhimmanci ba.

Kara karanta wannan

Za su sha mamaki"; Malamin addini ya hango abin da zai iya fariwa da Tinubu a 2027

Oyewole ya ce duk da cewa al’ummar Erinje sun yaba da tayin muƙamin da aka yi masa, mutane da dama na ganin bai yi daidai da irin goyon bayan da al’ummar suka bai wa gwamnan da APC ba.

‘Muƙamin tamkar cin mutunci ne’

Oyewole ya ce wasu daga cikin mutanen Erinje na kallon naɗin nasa a matsayin abin da bai nuna darajar goyon bayan da al’ummar suka bai wa gwamnatin Aiyedatiwa da APC ba.

“Wannan naɗin, duk da cewa muna godiya da shi, mutane da dama a cikin al’ummarmu suna kallonsa a matsayin cin mutunci, idan aka yi la’akari da irin gagarumin goyon baya da biyayyar da muka nuna wa gwamnatin ku da APC a Okitipupa da Jihar Ondo,” in ji shi.

Ya buƙaci muƙami mai gwabi ga Erinje

Oyewole ya roƙi Gwamna Aiyedatiwa da ya sake duba yadda ake rabon muƙaman siyasa a Erinje.

Ya kuma buƙaci gwamnan ya yi la’akari da naɗa ɗan asalin al’ummar Erinje zuwa wani babban muƙami na majalisar zartarwa ko wani muƙami na siyasa mai muhimmanci.

Jigon APC ya ki karbar mukami a Ondo
Taswirar jihar Ondo, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnonin APC na shirin hadewa da Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa akwai yiwuwar wasu gwamnonin jam'iyyar APC su hade da Atiku Abubakar.

Gwamnonin na APC da ba sa jin daɗin wasu al’amuran cikin gida na jam’iyyar sun fara tattaunawa kan yiwuwar kulla alaƙa da Atiku Abubakar gabanin babban zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng