An Gano Manyan Abubuwa 2 da Za Su Yi Tasiri a Zaben 2027
- Festus Okoye ya bayyana abubuwan da za su yi babban tasiri kan yadda za a gudanar da babban zaɓen 2027
- Tsohon kwamishinan INEC ya ce karuwar sayen ƙuri’u a rumfunan zaɓe na ƙara wahalar gano wa da dakile wannan matsala
- Okoye ya bukaci ’yan jarida su ƙara ilimin bincike da na doka domin su iya sa ’yan siyasa su ɗauki alhaki a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Tsohon kwamishinan ƙasa na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC), Festus Okoye, ya yi magana kan zaben 2027.
Festus Okoye ya ce sayen ƙuri’u a fili da rashin tsaro na iya yin babban tasiri kan zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Okoye ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 5 ga watan Satumban 2026 yayin wani taron koyar da ƙwarewa ta intanet da ƙungiyar Society of Nigerian Broadcasters (SNB), reshen Lagos, ta shirya, cewar rahoton jaridar TheCable.
Sayen ƙuri’u ya sauya salo
Tsohon kwamishinan INEC ya ce sayen ƙuri’u ya sauya daga yadda ake raba kuɗi a ɓoye ga masu zaɓe ƙarƙashin sunan shirye-shiryen tallafa wa jama’a.
A cewarsa, yanzu harkar ta ƙara fitowa fili, inda ’yan siyasa ke bai wa masu zaɓe kuɗi kai tsaye a wuraren da ake kaɗa ƙuri’a.
Okoye ya ce a wasu lokuta masu zaɓe na iya karɓar kuɗi daga ’yan siyasa daban-daban a wurin kaɗa ƙuri’a guda.
Ya ce hakan na ƙara wahalar gano matsalar da kuma ɗaukar matakan dakile sayen ƙuri’u yadda ya kamata.
Ya yi gargaɗi kan rashin tsaro
Okoye ya kuma bayyana damuwarsa kan matsalar tsaro da ka iya yin tasiri wajen gudanar da zaɓen 2027.
Ya ce yawan jami’an tsaro da kayan aiki da ake tura wa zaɓukan da ake gudanarwa a lokuta daban-daban a jihohi na iya zama ba za a iya maimaita shi a duk faɗin ƙasar ba yayin babban zaɓe.

Kara karanta wannan
Kungiyar 'yan gudun hijira a Kano ba ta son ganin Ali Modu Sheriff a gangamin yakin neman zaben APC
Tsohon kwamishinan ya ce wannan na iya zama babban ƙalubale, musamman a yankunan da tuni matsalar rashin tsaro ta yi ƙamari.
Yadda za a gudanar da zaɓe na cikin damuwa
Okoye ya ce halin da ake ciki na haifar da tambayoyi kan yadda za a gudanar da zaɓe da tattara sakamako a yankunan da rashin tsaro ya shafa a 2027.
Ya ce ya kamata hukumomin da abin ya shafa su fara yin la’akari da waɗannan matsalolin tun kafin lokacin zaɓe domin tabbatar da tsarin da zai ba ’yan ƙasa damar kaɗa ƙuri’unsu cikin aminci.
Ya soki yadda ake gudanar da zaɓen fidda gwani
Tsohon kwamishinan INEC ya kuma bayyana zaɓen fidda gwani na jam’iyyu a matsayin wani babban abin damuwa.
A cewarsa, yadda gwamnonin jihohi ke da ƙarfi wajen tafiyar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyu ya sa wasu ’yan siyasa ba su gamsu ba.
Ya ce rashin gamsuwar na sa wasu daga cikinsu neman wasu dandamalin siyasa domin cimma burinsu.

Source: Facebook
INEC za ta gudanar da zaben gwaji
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na duba yiwuwar gudanar da gwajin zaben shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.
Shugaban INEC ya ce hukumar na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da cikakken bincike kan tsarin fasahar zaɓe, yayin da shirye-shiryen gwajin zaben ke tafiya tare da tsarin kasafin kuɗin zaɓen.
Asali: Legit.ng
