Kungiyar 'yan gudun hijira a Kano ba ta son ganin Ali Modu Sheriff a gangamin yakin neman zaben APC
- Ƙungiyar jin daɗin ’yan gudun hijirar Borno da ke Kano ta roƙi APC ta sake duba shirin Ali Modu Sheriff halartar taron kamfen
- Ƙungiyar ta ce wasu mambobinta na ci gaba da ɗauke da raɗaɗin abubuwan da suka faru sakamakon rikicin Boko Haram a Borno
- ’Yan gudun hijirar sun jaddada cewa ƙin halartar Sheriff bai shafi goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Mambobin Ƙungiyar ’Yan Gudun Hijirar Borno da ke Kano sun roƙi kwamitin kamfen ɗin Shugaban Ƙasa na APC ya sake duba shirin tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, halartar wani taron kamfen.
An shirya gudanar da taron ne ranar Asabar a Kano, inda ƙungiyar ta nuna damuwa kan rahoton cewa Sheriff zai kasance cikin waɗanda za su halarta.

Source: Original
Ƙungiyar ta bayyana matsayinta ne a cikin wata wasiƙa da Legit Hausa ta samu mai ɗauke da ranar 4 ga Satumba 2026, wadda ta aika wa Darakta-Janar na Majalisar Kamfen ɗin Shugaban Ƙasa, Sanata Abdulazeez Yari.
Sun ce har yanzu suna goyon bayan Tinubu
Ƙungiyar ta jaddada cewa tana nan daram wajen goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma nasarar jam’iyyar APC.
Sai dai ta ce kasancewar Sheriff a wannan taro na iya jawo wa wasu daga cikin ’yan gudun hijirar Borno ciwo da tunanin abubuwan da suka faru a lokacin rikicin da ya tilasta musu barin garuruwansu.
Mambobin ƙungiyar sun ce da dama daga cikinsu sun tsere daga Borno zuwa Kano ne sakamakon hare-haren Boko Haram, kuma har yanzu suna ɗauke da raɗaɗin abubuwan da suka faru.
“A sake duba zuwansa taron”
Ƙungiyar ta ce kasancewar Sheriff a dandamalin APC a wannan lokaci na iya tayar da tsofaffin tunani masu raɗaɗi ga mutanen da suka rasa muhallansu.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Muna roƙon kwamitin kamfen cikin ladabi da ya sake duba shigarsa cikin wannan taro na musamman.”
A cewar ƙungiyar, bayyanar Sheriff na iya janye hankalin ’yan gudun hijirar daga saƙon haɗin kai sa kamfen ɗin ke son isarwa.
Ta kuma yi gargadin cewa kasancewarsa na iya sa wasu daga cikin ’yan gudun hijirar da ke shirin goyon bayan tikitin APC na shugaban ƙasa su ji an ware su.
Sun bambanta tsakanin Sheriff da Tinubu
Ƙungiyar ta yi ƙoƙarin fayyace cewa ƙin amincewarta da halartar Sheriff bai shafi goyon bayanta ga takarar Shugaba Tinubu ba.
Ta ce matsalar ita ce kasancewar Sheriff a wannan taro na musamman, ba wai ƙin goyon bayan gwamnatin Tinubu ko jam’iyyar APC ba.
Sun nemi Yari ya shiga tsakani
Ƙungiyar ta roƙi Abdulazeez Yari da ya shiga tsakani domin a sake duba batun, tana mai cewa tana da yakinin cewa zai yi amfani da matsayinsa wajen tabbatar da gudanar da kamfen cikin sauƙi.
Ta ce tana girmama jagorancinsa kuma tana fatan zai duba damuwar da ta bayyana kafin gudanar da taron.

Source: Facebook
Shugaban APC ya janye kalamansa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC mai mulki a jihar Yobe, Alhaji Mohammed Gadaka, ya janye kalaman da ya yi a baya tare da neman gafarar jama'a kan zaben 2027.
Ya janye maganar ne bayan shawara da ya ba wa matan aure da su rabu da mazansu idan har sun hana su zaɓen APC a zaɓe mai zuwa.
Asali: Legit.ng


