An Kara ba Tinubu Kariya kan Yunkurin Fitar da bayanansa na Hukumar FBI ta Amurka

An Kara ba Tinubu Kariya kan Yunkurin Fitar da bayanansa na Hukumar FBI ta Amurka

  • Wani jigo a APC, Olatunbosun Oyintiloye ya ce 'yan adawa na amfani da shari'ar FOIA da ta shafi Bola Tinubu a Amurka wajen yada farfaganda
  • Jigon APC ya ce shari'ar neman bayanai ba ta nufin an sake gurfanar da Tinubu kan wani laifi daban a kasar Amurka
  • Ya bukaci 'yan Najeriya su bambance tsakanin zargi, bincike, tuhuma da kuma hukuncin kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osogbo, Osun - Jigon APC a Osun, Olatunbosun Oyintiloye, ya zargi 'yan adawa da amfani da wata shari'a karkashin dokar neman bayanai ta Amurka (FOIA) da ta shafi Shugaba Bola Tinubu wajen neman biyan bukatunsu na siyasa.

Ya ce wasu 'yan adawa na amfani da ce-ce-ku-cen da suka taso kan shari'ar wajen yaudarar 'yan Najeriya domin samun galaba a siyasance gabanin babban zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya yi kaca kaca da yunkurin yan adawa na tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa 1 a 2027

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin taron kaddamar da ayyuka a Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Oyintiloye, tsohon dan majalisar dokoki, ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai ranar Lahadi a Osogbo, babban birnin jihar Osun, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Ya bayyana ma'anar shari'ar FOIA

Oyintiloye ya ce shari'ar da ke gaban wata kotu a Amurka shari'a ce ta neman samun damar duba wasu bayanai da hukumomin tsaron Amurka ke rike da su na Bola Tinubu.

Ya ce hakan ba yana nufin akwai wata shari'ar laifi ko kuma sake gurfanar da shugaban kasa Bola Tinubu a gaban kotu ba ne.

Ya ce:

"Shari'ar FOIA tana da alaka ne da neman damar samun bayanan gwamnati. Ba shari'ar laifi ba ce, ba sabuwsr shari'a ba ce kuma ba hukuncin kotu ba ne da ke bayyana mutum da laifi."

Jigon APC din ya ce babu wata kotu a Amurka da ta sake bude wata shari'ar laifi ko kuma ta bayar da umarnin sake shari'a kan Tinubu.

Kara karanta wannan

An kalubalanci Tinubu ya yi tafiya a mota idan ya gamsu da tsaro a Najeriya

Ya kara da cewa babu wani alkalin Amurka da ya taba bayyana shugaban kasar da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Ya yi magana kan bayanan FBI da DEA

Oyintiloye ya ce kasancewar wasu bayanai a hannun hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) ko hukumar yaki da miyagun kwayoyi (DEA) bai kamata a fassara hakan kai tsaye a matsayin hujjar aikata laifi ba.

A cewarsa, takardun bincike na iya kunshe da zarge-zargen da ba a tabbatar da su ba, wasu bayanan bincike ko kuma bayanan da wasu mutane suka bayar.

Jigon APC din ya bukaci 'yan Najeriya da kafafen yada labarai su guji abin da ya kira "yin hukunci da takardu kawai."

Ya ce zarge-zargen da ake yi wa Tinubu sun sha sake bayyana a wasu muhimman lokuta a tarihinsa na siyasa.

Ya kalubalanci jam'iyyun adawa

Oyintiloye ya zargi 'yan adawa da ci gaba da maimaita zarge-zargen da suka shafi kirkirar takardun karatu, aikata laifi da safarar miyagun kwayoyi.

Ya ce maimakon haka, ya kamata jam'iyyun adawa su gabatar wa 'yan Najeriya manufofi da shirye-shiryensu.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Sanatoci sun shiga damuwa da manyan sarakuna 2 suka rasu a Arewa

Bola Tinubu zai lashe zaben 2027

A wani labarin, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar PDP, Lere Olayinka, ya ce babban zaben shugaban kasa na shekarar 2027 zai fi wa Bola Ahmed Tinubu sauƙi fiye da zaben 2023.

Olayinka ya danganta hasashensa da kawancen siyasar da shugaban kasa ya kulla da wasu fitattun mutane, da kuma abin da ya bayyana a matsayin nasarar gwamnatin Tinubu wajen gudanar da mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262