Kurnkus: Fadar Shugaban Kasa Ya Fadi Dalilin Hana Futar da Bayanan Tinubu na Amurka
- Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da ya sa Bola Ahmed Tinubu ba ya son hukumomin Amurka su sako rahotonsa
- Fadar gwamnatin Najerirya ta ce Shugaba Tinubu ya yi amfani ne da kariyar sirri karkashin dokar Amurka
- Ta ce babu wata kotu ko hukumar Amurka da ta kama shugaban kasar da aikata wani laifi a cikin wannan shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi bayanin dalilin da ya sa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke adawa da fitar da wasu takardun bincikensa daga hukumomin tsaron Amurka.
Fadar shugaban kasar ta ce Tinubu ya dauki wannan matakin ne dogaro da hakkokin kariya da dokar FOIA ta Amurka ta tanada.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar yayin da ake ci gaba da muhawara kan batun, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Fadar shugaban kasa ta ce shari'ar da ke gaban Kotun Tarayya ta Amurka mai zaman kanta a District of Columbia rikici ne kan bukatar neman samun bayanan gwamnati.

Kara karanta wannan
Atiku ya nuna yadda kalaman IPMAN suka 'kunyata' Tinubu kan dawo da tallafin fetur a Najeriya
Ta jaddada cewa babu wata kotu ko hukumar gwamnatin Amurka da ta samu Tinubu da aikata wani laifi a cikin wannan shari'a.
Yadda rikicin ya fara a 2022
Fadar shugaban kasa ta ce batun ya samo asali ne tun shekarar 2022 lokacin da Aaron Greenspan ya gabatar da bukata karkashin dokar FOIA ga hukumomin gwamnatin Amurka daban-daban.
Greenspan ya nemi a ba shi wasu takardu da suka shafi Tinubu, wanda bayan hukimomin na Amurka sun ki yarda da suka ba da bayanan, Greenspan ya shigar da kara mai lamba 23-1816 a shekarar 2023.
An shigar da karar ne a gaban Kotun Tarayya ta Amurka mai zaman kanta a District of Columbia. Daga bisani kotun ta bai wa Tinubu damar shiga cikin shari'ar a matsayin wanda abin ya shafa kai tsaye.
An dauko batun wasikar Amurka ta 2003
Fadar shugaban kasa ta kuma tunatar da jama'a wata wasika da karamin ofishin jakadancin Amurka da ke Legas ya rubuta ranar 4 ga watan Fabrairun 2003.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauko batun abin da ya faru da Tinubu a 1993, ya aika sako fadar shugaban kasa
A cewar fadar shugaban kasa, binciken bayanan FBI da aka yi a lokacin bai gano wani tarihin kama Tinubu saboda laifi, wani sammacin kama shi ko sanarwar neman sa ba.
Ta ce hukumomin Amurka biyu da lamarin ya shafa su ne hukumar binciken manyan laifuka ta FBI da hukumar yaki da miyagun kwayoyi (DEA)
Sanarwar ta ce sun riga sun fitar da shafuka 399 na takardu bisa umarnin kotu, sai dai an boye wasu sassan bayanan bisa kebantattun tanade-tanaden dokar Amurka.
Greenspan ya kalubalanci matakin hukumomin na boye wasu sassan takardun.
A cewar fadar shugaban kasa, FBI da DEA, ta hannun Ma'aikatar Shari'a ta Amurka, sun yi adawa da bukatar fitar da takardun baki daya ba tare da boye komai ba bisa dalilai daban-daban na doka.
Dalilan kin fitar da wasu bayanan Tinubu
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilan da hukumomin Amurka suka bayar kamar haka:
- Bayanai da doka ta hana fitar da su ga jama'a, ciki har da bayanan shari'a da wasu bayanai kan na'urorin binciken karkashin FOIA Exemption 3
- Wasu takardu suna karkashin kariyar sirrin alaka tsakanin lauya da wanda yake karewa, da kuma takardun aikin lauya karkashin FOIA Exemption 5
- Wasu bayanai an shirya su ne domin ayyukan binciken laifuffuka kuma dokar FOIA ta ba su kariya
- Wasu takardu na dauke da bayanan da fitar da su zai iya shiga cikin sirrin mutane ba tare da dalili ba karkashin FOIA Exemptions 6 da 7(C)
- Wasu bayanai na iya tona asirin masu bayar da bayanan sirri ko hanyoyin binciken hukumomin tsaro, wanda ke karkashin FOIA Exemptions 7(D) da 7(E)

Kara karanta wannan
Zance ya kare, Amurka ta gudanar da bincike kan zargin Tinubu da safarar miyagun kwayoyi
Tinubu ya dogara da kariyar sirri
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu, bisa shawarar lauyoyinsa, ya kuma yi amfani da hakkinsa karkashin FOIA Exemption 7(C). Wannan tanadi yana kare bayanan sirrin mutum da ke cikin wasu takardun hukumomin binciken laifuffuka.
Fadar shugaban kasar ta jaddada cewa matakin shugaban kasar na neman kariyar bayanansa bai kamata a fassara shi a matsayin amincewa da aikata wani laifi ba.
Ta ce batun da ake yi yanzu ya ta'allaka ne kan iyakar bayanan da dokar Amurka ta halatta a fitar ga jama'a.
Asali: Legit.ng