‘Abin da Ya Sa Amurka ba Za Ta Cafke Tinubu a Taron Majalisar Dinkin Duniya’
- Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Shugaba Tinubu ba zai fuskanci kamu ba a Amurka
- Ya ce yarjejeniyar 1947 tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Amurka ta kare shugabannin ƙasashe da iyalansu
- Ibrahim ya bayyana cewa zargin aikata laifi kaɗai bai isa a hukunta mutum ba, domin dole ne a tabbatar da zargin ta hanyar doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Ambassada Jimoh Ibrahim, ya yi magana kan zargin shirin kama Bola Tinubu a Amurka.
Sanata Jimoh ya ce Shugaba Bola Tinubu da iyalansa suna da damar zirga-zirga ba tare da cikas ba.

Source: Twitter
Ibrahim, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan Kasafin Kuɗi da Harkokin Gudanarwa, ya ce Amurka ba ta sanar da Ofishin Jakadancin Najeriya takunkumi ba, cewar The Nation.
'Babu wani tabbacin shirin cafke Tinubu'
Ya ce ba a sanar da Najeriya wani ƙuntatawa da gwamnatin Amurka ta sanya kan zirga-zirgar Shugaba Tinubu yayin taron Majalisar Dinkin Duniya na UNGA ba.
Ibrahim ya yi nuni da Sashe na 11 na Yarjejeniyar 1947 tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Amurka, yana mai cewa halartar taron ya danganta da bukatun ƙasa.
Ya bayyana cewa sama da kashi 60 cikin 100 na jerin waɗanda za su gabatar da jawabai a taron na bana sun ƙunshi mataimakan shugabannin ƙasashe da ministocin harkokin wajen ƙasashe.
A cewarsa, a irin wannan yanayi, shugaban ƙasa na iya wakilta wani jami’i domin ya wakilce shi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, cewar Punch.
Ibrahim ya ƙara bayyana cewa ƙasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya ne ake gayyata domin su halarci babban taron, ba wai shugabanninsu ake gayyata da kansu ba.
Ya ce Sashe na 11 na yarjejeniyar 1947 ya tanadi kariya ga wakilan ƙasashe mambobi da iyalansu daga duk wani cikas yayin tafiyarsu zuwa ko daga yankin hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya.

Source: Facebook
Abin da ya kamata Amurka ta yi
Ya bayyana cewa wannan tanadi yana bukatar gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomin Amurka su guji sanya duk wani cikas ga zirga-zirgar wakilan ƙasashe mambobi da iyalansu.
Haka kuma, ya ce kariyar ta shafi jami’an Majalisar Dinkin Duniya da hukumominta na musamman, da kuma mutanen da aka gayyata zuwa hedikwatar domin gudanar da ayyukan hukuma.
Jakadan ya kuma bayyana cewa wani tsohon shugaban Najeriya, wanda ba Bola Tinubu ba ne, ya taɓa fuskantar ƙuntatawa ta yadda ba zai iya wuce kilomita 10 daga hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya ba.
Ya ce wannan ƙuntatawa ta faru ne a lokacin da tsohon shugaban ke halartar taron UNGA, sakamakon wata magana da ta shafi harkar miyagun ƙwayoyi.
Gwamnatin Najeriya ta magantu kan makamin nukiliya
A wani labarin, an ji cewa Jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Najeriya ba ta mallaki makaman nukiliya ba.
Jimoh Ibrahim ya bukaci a sake duba dokar Majalisar Dinkin Duniya kan rashin tsoma baki idan ƙasa na gwajin makaman nukiliya.
Ya ce Najeriya na haɗin gwiwa da ƙasashe daban-daban wajen ƙarfafa ƙoƙarin duniya na kawar da gwajin makaman nukiliya.
Asali: Legit.ng


