An Kalubalanci Tinubu Ya Yi Tafiya a Mota Idan ya Gamsu da Tsaro a Najeriya
- Jam'iyyar APM ta kalubalanci shugaban kasa Tinubu da ministan tsaro Gen. Christopher Musa (retd.) su yi tafiya a kan hanya ba tare da dakaru ba
- Jam'iyyar ta mayar da martani ne kan kalaman ministan da ya ce an murkushe 'yan ta'adda kuma sace mutane a yanzu ya koma wata matsalar zamantakewa
- Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Abubakar Yusuf, ya ce gwamnatin na tsallake gaskiya ne kawai game da matsalar tsaro a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Jam'iyyar APM ta kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Ministan Tsaro, Gen. Christopher Musa (retd.), da sauran manyan jami'an gwamnati da su yi tafiyar mota a kan hanya ba tare da jami'an tsaro ba idan har da gaske tsaro ya inganta.
Jam'iyyar ta fitar da wannan kalubale ne a ranar Asabar a birnin Abuja yayin da take maida martani kan ikirarin da Musa ya yi kwanan nan na cewa Gwamnatin Tarayya ta "ci galaba kan 'yan ta'adda" kuma sace mutane ya zama wata matsalar zamantakewa maimakon babbar matsalar tsaro.

Kara karanta wannan
2027: Jam'iyyar NDC ta su Kwankwaso ta fitar da sunayen yan takarar gwamna a jihohi 12
Sakataren yada labaran jam'iyyar ta APM na kasa, Mr Abubakar Yusuf, ya zargi gwamnatin Tinubu da rayuwar karya kan ainihin halin da ake ciki, inda ya bayyana cewa abin da ke faruwa a kasa ya saba da da'awar gwamnatin.

Source: Facebook
Abin da Jam'iyyar APM ke cewa
Da yake martani kan yadda tsaro yake a Najeriya, Yusuf ya ce:
"Idan har tsaro ya inganta kamar yadda gwamnatin ke ikirari, APM tana kalubalantar Shugaban Kasa, Ministan Tsaro da sauran manyan jami'an fadar shugaban kasa da su yi tafiyar mota ba tare da jami'an tsaro ba kamar yadda sauran 'yan Najeriya ke yi."
'Yan Najeriya da dama sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda gwamnatin kasar ke ci gaba da magana kan ingancin tsaro, inda a har yanzu ake fama da matsanancin rashin tsaro.
Batun da ya tada kura a Najeriya
Minista Musa, yayin da yake magana a wata hira da gidan talabijin a ranar Talata, ya ce gwamnati ta sami nasarori wajen yakar ta'addanci kuma matsalar ta ragu.
A cewarsa:
"Gaskiya ne cewa munci galaba kan 'yan ta'adda saboda yanzu hare-haren ba su da yawa, abin da ake fama da shi yanzu shi ne sace mutane.

Kara karanta wannan
"Ka yi yadda na yi," Atiku ya sake kinkimo magana mai girma kan bayanan Tinubu na Amurka
"Sace mutane wata matsala ce ta zamantakewa inda yanzu za ka ga mata na sace mazajensu ko maza na sace 'ya'yansu."
Ministan ya ci gaba da cewa:
"Ina tabbatar muku cewa tsaro ya inganta. Watakila ka lura cewa ba ka cika jin hare-haren Boko Haram ko ISWAP a ko'ina ba, sai dai jifa-jifa."
Ana zaman dar-dar a Najeriya
Sai dai, a zahirin gaskiya tsaro bai inganta ba a Najeriya, saboda har yanzu 'yan kasar na ci gaba da zaman dar-dar a kusan dukkan yankunan kasar.
Wakilin Legit.ng Hausa ya tattauna da wata 'yar kasuwa mai gudanar da hada-hadar saye da sayarwa tsakanin Gombe da Taraba, Sadiya Muhammad, inda ta shaida mana cewa:
"Gaskiya tsaro kam babu a Najeriya. Kullum idan na hau mota a Gombe zan tafi Taraba hankali na a tashe yake don ban san me zai faru ba. Fatanmu Allah ya kawo mana sauki cikin gaggawa."
Atiku ya sha alwashin kawo tsaro
A bangare guda, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa na tabbatar da tsaro a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da BBC Hausa, inda ya kushe wasu manufofin gwamnatin Tinubu.
Ya kuma yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi jin dadin 'yan kasa, ciki har da dawo da tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng
