Duk da Shirin Hadakar Yan Adawa, Jigon PDP Ya Sallama Wa Shugaba Tinubu a Zaben 2027

Duk da Shirin Hadakar Yan Adawa, Jigon PDP Ya Sallama Wa Shugaba Tinubu a Zaben 2027

  • LLere Olayinka ya ce shugaban kasa Bola Tinubu zai samu sauƙin lashe zaben 2027 fiye da yadda ya samu a 2023
  • Jigon PDP ya danganta hakan da yadda Tinubu ya kulla alaka da wasu fitattun 'yan adawa da kuma salon tafiyar da siyasa
  • Olayinka ya ce kasancewar Nyesom Wike tare da gwamnatin Tinubu ya rage wa PDP damar tara ƙarin magoya baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani jigo a jam'iyyar PDP, Lere Olayinka, ya ce babban zaben shugaban kasa na shekarar 2027 zai fi wa Bola Ahmed Tinubu sauƙi fiye da zaben 2023.

Olayinka ya danganta hasashensa da kawancen siyasar da shugaban kasa ya kulla da wasu fitattun mutane, da kuma abin da ya bayyana a matsayin nasarar gwamnatin Tinubu wajen gudanar da mulki.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya yi kaca kaca da yunkurin yan adawa na tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa 1 a 2027

Lere Olayinka.
Jigo a jam'iyyar adawa ta PDP, Lere Olayinka Hoto: Lere Olayinka
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi ranar Litinin, inda ya ce Tinubu ya samu nasarar jawo wasu manyan jiga-jigan 'yan adawa zuwa bangaren gwamnatinsa.

Olayinka ya yi hasashen nasarar Tinubu

A cewarsa, dabarun siyasar shugaban kasa sun sanya tazarar samun nasara a zaben 2027 ta zama mai sauƙi idan aka kwatanta da abin da ya faru a 2023.

Ya ce:

"Dalilin da ya sa zaben 2027 zai zama zabe mai tafiya hanya guda shi ne saboda yadda shugaban kasa ya yi aiki wajen ci gaban kasa da kuma salon siyasarsa, domin wannan zabe zai zama mafi sauƙi.
"Zai fi wa shugaban kasa sauƙi fiye da zaben 2023. Wannan gaskiya ce da mutane da yawa ba sa son su amince da ita."

Ya ambaci tasirin Nyesom Wike

Olayinka ya yi nuni musamman da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, wanda har yanzu mamba ne na PDP amma yake aiki tare da gwamnatin Tinubu.

Kara karanta wannan

Tinubu bai cire kansa ba, ya faɗi irin shugabannin da Najeriya ke buƙata

Ya ce da Wike bai mara wa gwamnatin shugaban kasa baya ba, da watakila ya yi amfani da karfinsa wajen kara wa PDP magoya baya.

Ya ce:

"Da Wike ba ya aiki tare da shugaban kasa, da watakila ya tara karin goyon baya ga PDP. Amma yanzu ba haka lamarin yake ba. Shugaban kasa ya samu damar jawo shi da wasu mutane zuwa bangarensa."
Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin tarayya Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Olayinka ya ce yadda Tinubu ke nuna niyyar aiki da mutane daga bangarorin siyasa daban-daban ya sauƙaƙa masa yanayin siyasa tare da rage karfin 'yan adawa wajen tara magoya baya.

Olayinka ya kuma bukaci 'yan Najeriya su amince da irin goyon bayan da Wike ke ba Tinubu, duk da cewa ministan babban birnin tarayya har yanzu mamba ne na jam'iyyar PDP mai adawa.

Tompolo ya fara tallata Tinubu a Katsina

Kun ji cewa attajirin Kudancin Najeriya da aka sani da Tompolo, ya kaddamar kungiyar tallata Bola Tinubu a jihar Katsina domin tara goyon bayan jama’a ga sake zabensa a 2027.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a People’s Square da ke Katsina, inda aka nada masu kula da kungiyar a kananan hukumomi 34 tare da mika musu motocin yakin neman zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262