Najeriya Ta Yi Rashi: Sanatoci Sun Shiga Damuwa da Manyan Sarakuna 2 Suka Rasu a Arewa

Najeriya Ta Yi Rashi: Sanatoci Sun Shiga Damuwa da Manyan Sarakuna 2 Suka Rasu a Arewa

  • Sanatoci daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja sun mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar manyan sarakuna biyu a Zamfara da Jigawa
  • Shugaban kungiyar sanatocin Arewa, Abdul'aziz Musa Yar'adua ya ce rasuwar Sarkin Gumel da Sarkin Zurmi babban rashi ne ga kasa baki daya
  • Kungiyar ta mika sakon ta'aziyya ga Majalisun Masarautun Gumel da Zurmi, iyalan mamatan, da gwamnatoci da al'ummar jihohin Jigawa da Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanatoci daga jihohin Arewa 19 da Abuja, karkashin kungiyarsu ta NSF, sun yi alhinin rasuwar Sarkin Gumel, Dr. Ahmed Muhammad Sani da Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman.

'Yan majalisar dattawan sun bayyana rasuwar sarakunan biyu a matsayin babban rashi ga masarautu da al'ummar yankunansu, suna masu cewa sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban al'umma.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ware gwamnonin Arewa, ya fadi matsalan da za su fuskanta a zaben 2027

Sarkin Zamfaran Zurmi.
Mai Martaba sarkin Zamfaran Zurmi, Marigayi Alhaji Bello Sulaiman Hoto: Masarautar Gusau
Source: Facebook

Sarkin Gumel ya rasu a ranar 3 ga watan Satumban 2026, yayin da Sarkin Zurmi ya rasu a ranar Litinin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cikin sakon ta'aziyyar da shugaban kungiyar sanatocin Arewa, Sanata Abdulaziz Musa Yar'Adua, ya sanya wa hannu, sun bayyana irin gudunmawar da sarakunan biyu suka bayar ga al'ummominsu da yankin Arewa baki daya.

Ta'aziyyar rasuwar Sarkin Gumel

Sanatocin sun bayyana marigayi Sarkin Gumel a matsayin masani kuma gogaggen mai gudanarwa wanda ya inganta ilimi da zaman lafiya a tsawon mulkinsa.

Sun ce ya karfafa ilimin 'ya'ya mata tare da amfani da matsayinsa wajen bunkasa hadin kai tsakanin al'ummomi da kabilu daban-daban.

'Yan majalisar sun kuma yabawa marigayi Sarkin Zurmi bisa jajircewarsa wajen jagorantar masarautarsa a lokacin da Zamfara ke fuskantar matsalolin tsaro.

A cewarsu, shekaru biyar da ya shafe yana kan karagar mulki sun kasance cike da kokarin samar da zaman lafiya, hadin kai da juriya tsakanin al'ummar Masarautar Zurmi.

Kara karanta wannan

Christopher Musa ya yi wa Kwankwaso da Obi raddi, ya ce Tinubu zai zarce

Sanatocin sun ce sarakunan biyu sun wuce iyakacin nauyin da sarautarsu ta dora musu, inda suka yi amfani da matsayinsu wajen inganta zaman lafiya, fahimtar juna da ci gaba.

Sanarwar ta ce:

"Za mu ci gaba da tuna Dr. Ahmed Muhammad Sani, CON, a matsayin masani, mai tawali'u kuma mai hada kan jama'a wanda ya rike sarautar Gumel cikin tawali'u, hikima da mutunci.
Gumel.
Mai martaba Sarkin Gumel na jihar Jigawa, Dr Ahmed Muhammad Sani Hoto: Masarautar Gumel
Source: Facebook

Ta'aziyyar rasuwar Sarkin Zurmi

Dangane da marigayi Sarkin Zurmi, sanatocin sun ce:

"A cikin shekaru biyar da ya shafe a kan karagar mulki, ya nuna jarumtaka da kyakkyawan shugabanci, inda ya karfafa zaman lafiya, hadin kai da juriya a Masarautar Zurmi.

Kungiyar ta mika sakon ta'aziyya ga Majalisun Masarautun Gumel da Zurmi, iyalan mamatan, da gwamnatoci da al'ummar jihohin Jigawa da Zamfara.

Sanatocin sun roki Allah Madaukakin Sarki ya gafarta kura-kuran mamatan, ya karbi kyawawan ayyukansu tare da saka su a Aljannatul Firdaus, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Gwamna Namadi ya yi ta'aziyyar Sarkin Gumel

Kun ji cewa Gwamna Umar Namadi ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani II, a matsayin babban rashi ga jihar Jigawa.

Gwamna Namadi ya bayyana hakan ne ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Bala Ibrahim, yayin da yake ganawa da manema labarai kan rasuwar Sarkin a ofishinsa da ke Dutse.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262