An Rage Mugun Iri a Arewa, Hatsabibin Dan Bindiga Ya Bakunci Lahira a Zamfara

An Rage Mugun Iri a Arewa, Hatsabibin Dan Bindiga Ya Bakunci Lahira a Zamfara

  • Shahararren ɗan bindiga Kachalla Auta, wanda ya addabi al’ummomin Zurmi, ya mutu yayin arangama da jami’an tsaro a Zamfara
  • Dakarun tsaro sun yi wa mayakan Auta kwanton-bauna, inda aka kashe wasu tare da kwato babura kafin sake fafatawa da su
  • An kashe Auta a arangamar Boko–Moriki, lamarin da zai zama babban koma-baya ga ƙungiyarsa da ayyukan ta’addanci yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zamfara - Al'ummar wasu yankuna a jihar Zamfara sun samu sauki bayan hallaka daya daga cikin hatsabiban yan bindiga wanda ya kasance mai hatsari a yankin.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa wani daga cikin manyan yan bindiga, Kachalla Auta ya mutu yayin arangama da jami'an tsaro.

An kashe hatsabibin dan bindiga a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke fama da matsalar tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Bakatsina da ke kawo bayanai kan tsaro ya ce dan bindigan ya dade yana addabar al’ummomin Zurmi da ke jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Shugaban da ya nemi mata su kashe aurensu kan zaben APC ya magantu

Galabar da jami'an tsaro ke samu a Zamfara

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun nasara kan yan bindiga bayan cafke wasu daga cikin masu taimaka masu ta hanyoyi da dama.

Askarawan Zamfara sun gabatar da mutane tara da aka kama bisa zargin kasancewa ’yan bindiga, masu leƙen asiri da masu samar da kayan aiki.

Wani matashi mai shekaru 20 ya amsa cewa ya shafe watanni a sansanin fitaccen ɗan bindiga Kachalla Gwaska, inda ya shiga ayyuka a jihohi da ƙasashe daban-daban.

Rundunar ta ce sama da Naira miliyan 226 aka karɓa a matsayin kuɗin fansa daga sace-sacen da ake zargin waɗanda aka kama sun gudanar.

An kashe dan bindiga a Zamfara
Marigayi Kachallah Auta da Gwamna Dauda Lawal. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Source: Facebook

Yadda jami'an tsaro suka yi masu bazata

A daren jiya, jami’an tsaro sun yi wa mayakan Auta kwanton-bauna, inda rahotanni suka ce an kashe da dama daga cikinsu tare da kwato babura.

Da safiyar yau, ƙungiyar ta sake bayyana a yankin hanyar Boko–Moriki, inda dakarun tsaro suka sake fafatawa da su cikin wani mummunan musayar wuta.

Kara karanta wannan

Sirrin yadda sojoji ke ceto mutane a daji ba tare da kashe 'yan ta'adda ba

Rahotanni sun ce Kachalla Auta na cikin ’yan bindigar da aka kashe yayin wannan samame da jami’an tsaro suka gudanar a yankin.

Mutuwar Auta za ta iya zama babban koma-baya ga ƙungiyarsa, musamman wajen ci gaba da ayyukan ta’addanci da sauran hare-harensu a yankin.

Wannan nasara ta nuna ƙoƙarin jami’an tsaron Najeriya na ci gaba da matsa lamba tare da fuskantar ƙungiyoyin ’yan bindiga kai tsaye a filin daga.

Ado Aleiro ya rasa dansa a gumurzu

A wani labarin, mun kawo muku rahoton cewa hatsabibin dan bindiga, Ado Aleiro ya gamu da cikas yayin da aka yi arangama da miyagu a jihar Katsina.

Aleiro ya rasa ɗansa da wasu ’yan uwansa takwas, yayin da aka lalata babura kusan 30 na ƙungiyarsa a wani artabu a Katsina.

Rahotannin leƙen asiri sun ce asarar ta raunana bangaren Aleiro, tare da rage masa damar zirga-zirga, sadarwa wanda ake ganin zai yi tasiri a yaƙi da ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.