‘Dan Takarar Shugaban kasa a PRP Ya Ce Gara Mulkin Soja da Tsarin Yau
- Donald Duke bai ganin an samu wani canji daga lokacin Shehu Shagari zuwa yanzu ta fuskar karfin tattalin arziki a Najeriya
- Ya ce halin ƙunci da talauci da mutane ke ciki ya haifar da Boko Haram, 'yan bindiga, da masu garkuwa da jama’a a kasar
- Mista Duke yana so gwamnati ta daina auna nasarar tattalin arziki da yawan ajiyar kuɗin ƙaje, ta duba yawan masu abin yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Donald Duke mai fatan ‘yan Najeriya su zabe shi ya zama shugaban kasa a takarar 2027 ya kushe tsarin mulkin da ake yi.
‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar PRP mai adawa ya ce abubuwa sun fi yi wa ‘yan Najeriya kyau a shekarar 1999 a kan yanzu.

Source: Facebook
Donald Duke ya kushe dimokuradiyyar Najeriya
Duk da ana karkashin mulkin farar hula, jaridar This Day ta rahoto Donald Duke yana nuna al’umma ba su morar tsarin yadda ya kamata.
An samu shugabannin farar hula sun mulki kasar Najeriya daga 1999 zuwa yau bayan Janar Abdulsalami Abubakar ya shirya zabe.
Duke ya shiga cikin muhawarar da ake yi game da tsarin da ya fi amfanar da Najeriya tsakanin mulkin sojoji da gwamnatin farar hula.
Da dimokuradiyya da soja wanne ya fi?
Amma shi Duke bai ma ganin cewa ana bin tsarin damukaradiyya na gaskiya a kasar ganin matsalolin tattalin arziki da ake fama da su.
"Ba a tsarin damukaradiyya mu ke ba. Duk buge ce. Kuma duk gwamnatin ta zo, kara tsiyacewa mu ke yi.
"Zan iya fada maka karara cewa abubuwan sun yi yi wa mutane kyau a 1999 a kan yau a 2026.
"Mutane sun fi jin dadi (a lokacin). Kasar ta fi saukin rayuwa.
- Donald Duke
Duke: Najeriya ba ta samu cigaban tattalin arziki ba
The cable ta rahoto shi ya ce a mulkin Shehu Shagari, ana yin kasafin $25bn a shekara, sa’ilin da mutane ba su wuce miliyan 70 ba.
Amma har yanzu da adadin jama’a ya zarce miliyan 200, Duke ya ce kasafin kudin bai karu ba idan ana lissafi ne da dalar kasar Amurka.
Ana ambatar cewa gwamnatin Najeriya za ta kashe tiriliyoyi a shekara, amma a zahiri an karya darajar Naira daga N1 zuwa N1400 kan dala.
A bangaren tsaro, ya koka da matsalar Boko Haram da ‘yan bindiga, yana mai cewa raunin tattalin arziki ya jawo bullar ‘yan ta’adda a kasar nan.
‘Dan siyasar ya kuma bukaci a rage masu zaman kashe wando, ya kuma ce idan ana so a ga cigaba, ya zama wajibi a ba ilmi muhimmanci.
Bai ganin nasarorin hakika suna cikin alkaluman tattalin arziki irinsu karfin asusun ajiyar kudin waje.

Source: Getty Images
Atiku ya zargi Tinubu da tsiyata jama'a
An ji Atiku Abubakar ya sake sukar Bola Tinubu, ya ce tsare-tsaren tallafinsa sun fifita abokan kasuwancinsa da manyan kamfanonin mai ne.
'Dan adawan ya zargi Bola Ahmed Tinubu da jefa mutane a talauci da aka cire tallafin fetur a sanadiyyar tsadar sufuri da kaya a kasuwanni.
Atiku Abubakar ya ce duk yadda ake ikirarin alkaluma sun yi kyau, mutane suna wayyo Allah a mulkin APC kuma sun gaji da yin hakuri.
Asali: Legit.ng

