Mala Buni zai cigaba da aiki da Malam Wali a matsayin SSG

Mala Buni zai cigaba da aiki da Malam Wali a matsayin SSG

Mun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin jihar Yobe a karkashin gwamna Ibrahim Gaidam watau Alhaji Baba Mallam Wali mni, zai cigaba da rike wannan mukami a matsayin rikon kwarya har yanzu.

Sabon gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya zabi Baba Mallam Wali ya rike ofishin mukaddashin Sakataren gwamnatin jihar har zuwa lokacin da zai nada wanda zai rike mukami.

Sabon gwamnan ya sanar da wannan ne tun jiya 2 ga Watan Mayu, bayan an rantsar da shi a matsayin zababben gwamnan jihar Yobe. Mala Buni ya zabi ya cigaba da aiki da SSG din tsohon gwamna.

Alhaji Baba Mallam Wali mai shekara 50 a Duniya ya fito ne daga Garin Nguru, inda yayi Firamare da Sakandare, Daga baya Baba Wali ya tafi jami’ar ABU ta Zaria yayi Digirin farko da na biyu.

KU KARANTA: Ba zan iya biyan Ma'aikata N30 , 000 ba - Makinde

Wali ya kammala jami’a ne shekaru fiye da 35 da su ka wuce inda ya karanci ilmin raye birane. SSG din yayi aiki da hukumar da ke kula da tafkin Chad a 1982, daga baya ya koma gwamnatin tarayya.

Sakataren gwamnatin ya kuma yi aiki a irin su hukumar MAMSER da sauran su a lokacin mulkin Babangida, tun jihar Yobe na hade da Borno. Wali ya kuma rike mukami a hukumar NEAZDP ta Arewa ta gabas.

A da, Malam Wali yayi aiki da hukumar nan ta NAPEP da gwamnatin Obasanjo ta kafa. Bayan nan ne ya dawo jihar Yobe ya rike Darekta zuwa Darektan din-din-din a shekarar 2007 a ma’aikatu da-dama.

Ibrahim Gaidam ne ya fara nada Malam Wali Sakataren Gwamnati a lokacin yana gwamna. Yanzu sabon gwamnan jihar zai yi aiki da shi har zuwa lokacin da aka nada takamaimen SSG inji Abdullahi Bego.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel