Rashin Tsaro: Janar Musa Ya ce Najeriya Ta Yi Galaba kan 'Yan Ta'adda, Ya Gabatar da Dalili

Rashin Tsaro: Janar Musa Ya ce Najeriya Ta Yi Galaba kan 'Yan Ta'adda, Ya Gabatar da Dalili

  • Christopher Musa ya ce gwamnatin tarayya ta yi galaba kan ’yan ta’adda, yana mai cewa hare-haren Boko Haram da ISWAP sun ragu sosai idan aka kwatanta da baya
  • Ministan ya ce ’yan ta’adda sun koma yin garkuwa da mutane domin samun kuɗi, yayin da sojoji ke shiga maboyarsu tare da kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su
  • Janar Musa ya ce kasancewarsa cikin tawagar yaƙin neman zaɓen APC ba zai shafi aikinsa na ministan tsaro ba, yana mai cewa zai tabbatar da zaɓe cikin ’yanci da gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce gwamnatin tarayya ta yi galaba kan ta’addanci a Najeriya.

Janar Musa ya ce hare-haren ’yan ta’adda ba su sake kasancewa cikin tsananin da suka kasance a baya ba, yayin da matsalar garkuwa da mutane ta fi bayyana a yanzu.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya gargadi gwamnoni kan raba babura, ya fadi illar haka ga tsaro

Christopher Musa ya ce an yi galaba kan 'yan ta'adda
Janar Christopher Musa na jawabi a wajen taro Hoto: Ministry of Defence Nigeria
Source: Facebook

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 3 ga watan Satumban 2026 yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Tv.

Hare-haren Boko Haram da ISWAP sun ragu

Da aka tambaye shi ko Najeriya ta yi galaba kan ’yan ta’adda ne ko kuma kawai an tarwatsa su zuwa wasu wurare, Janar Musa ya ce gwamnati ta yi galaba a kansu.

"A gaskiya, mun yi galaba a kansu saboda yanzu, kamar yadda na fada, hare-haren ba su da yawa kamar da, kuma abin da ya fi yawa yanzu shi ne garkuwa da mutane.” In ji shi.

Tsohon babban hafsan tsaron ya ce yanayin tsaro ya inganta a Najeriya a ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu.

Ya ce rahotannin hare-haren Boko Haram da ISWAP ba sa yawaita kamar yadda suke a baya.

’Yan ta’adda sun koma garkuwa da mutane

Janar Musa ya bayyana yadda matsalar laifuffuka ke sauyawa daga wani mataki zuwa wani, yana mai cewa idan jami’an tsaro suka matsa wa masu aikata laifuffuka, sukan koma wata hanya mafi sauƙi ta samun kuɗi.

Kara karanta wannan

Kwamishina ya yi amai ya lashe kan barazana ga masu adawa da APC

"Daga aikata laifi zuwa garkuwa da mutane, zuwa ta’addanci da tayar da ƙayar baya; idan ka iya matsa musu, sai abin ya yi ƙasa.” In ji shi.

A cewarsa, yanzu masu aikata laifuffukan sun koma garkuwa da mutane saboda hanya ce mafi sauƙi da suke amfani da ita wajen tara kuɗi.

Ministan ya ce yanzu sojoji suna shiga cikin maboyar ’yan ta’adda tare da kubutar da mutane da dama da aka yi garkuwa da su.

Janar Musa ya yi magana kan zaɓen 2027.

Janar Musa ya ce matsalar rashin tsaro ba za ta yi tasiri ga yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ba.

Ya kuma kare kasancewarsa cikin tawagar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta APC da ke kula da harkokin tsaro.

Christopher Musa ya yi magana kan rashin tsaro
Janar Christopher Musa zaune a wajen taro Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Janar Musa ya yi zarge-zarge kan El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaro, Christopher Musa, ya fito fili ya zargi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Ministan tsaron ya zargi tsohon gwamnan na Kaduna da aikata abubuwa marasa kyau wadanda suka haifar da rabuwar kai mai tsanani a tsakanin al'umar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng