Kwankwaso Ya Ware Gwamnonin Arewa, Ya Ce Za Su Sha Wahala a Zaben 2027

Kwankwaso Ya Ware Gwamnonin Arewa, Ya Ce Za Su Sha Wahala a Zaben 2027

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce wasu gwamnoni, musamman na Arewacin Najeriya, sun gaza matuka har zai yi musu wahala su fita neman kuri'u
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce rashin tsaro da zargin rashin amfani da kudaden gwamnati yadda ya kamata sun kara fusata 'yan Najeriya
  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC ya tuna yadda shugaban kasa mai ci ya fadi zabe duk da yana kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya yi garhadin cewa yan Najeriya sun fusata da wasu daga cikin shugabanninsu musamnan gwamnonj.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin taron jam'iyyarsu ta NDC da aka gudanar a jihar Rivers ranar Alhamis da ta gabata.

Kwankwaso.
Dan takarar mataimakin shugaba kasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

A rahoton Leadership, tsohon gwamnan jihar Kano ya ce gwamnoni da dama, musamman wadanda ke Arewacin Najeriya, sun yi abin da ya bayyana a matsayin rashin kyakkyawan aiki da gazawa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ministan tsaro ya yi zarge zarge kan El Rufa'i da ke tsare

Kwankwaso ya yi hasashen cewa irin wadannan gwamnoni na jihohin Arewa zai yi musu wahala su fito neman kuri'a domin samun nasarar jam'iyyarsu a zaben 2027.

Wani mai amfani da manhajar X mai suna ChuksEricE ne ya wallafa bidiyon taron.

Ya soki ayyukan gwamnonin Arewa

Kwankwaso ya yi hasashen cewa gwamnoni da dama, musamman na Arewacin Najeriya, za su fuskanci fushin jama'a wajen fita neman kuri'u domin jam'iyyunsu.

Ya ce abin da ya gani daga yadda abubuwa ke tafiya ya nuna cewa wasu gwamnoni da jam'iyyunsu ba su yi abin da ya kamata ba.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC ya kuma soki yadda gwamnonin jihohi da gwamnatin tarayya ke tafiyar da kudaden jama'a.

Kwankwaso ya yi maganar kudaden gwamnati

Ya ce kasar Najeriya na samun kudade masu yawa fiye da shekarun baya sakamakon cire tallafin mai, amma ba a tafiyar da su yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi amfani da gwamnoni 30, ya yi maganar da za ta tsorata Tinubu kan zaben 2027

Ya ce:

“Yanzu cikin shekara guda, mun gani a kafafen sada zumunta cewa gwamnatinmu ta tara sama da Naira tiriliyan 1.11 cikin kasa da shekara guda. Ka zagaya ka gani, me aka yi da wannan kudin? Kusan babu komai.”

Yadda yan Najeriya suka fusata

Kwankwaso ya ce abin da ya bayyana a matsayin rashin kyakkyawan aikin gwamnatoci ya kara fusata 'yan Najeriya.

Ya kara da cewa matsalar rashin tsaro na daga cikin manyan abubuwan da ke damun jama'a, musamman a Arewacin Najeriya.

A cewarsa:

“Mutane suna cikin fushi sosai. Wannan fushin ba abu ne mai kyau ba, sannan abin da ya fi muni shi ne matsalar rashin tsaro, musamman a Arewacin Najeriya.”

Kwankwaso ya gargadi APC kan gwamnoni

A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso ya ce yawan gwamnoni da jam'iyya ke da su ba tabbacin lashe zaben 2027 ba ne.

Kwankwaso ya ce tarihin zabukan da suka gabata ya nuna cewa gwamnati mai ci na iya rasa zabe duk da kasancewarta mai iko da jihohi da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262