INEC Za Ta Fitar da Sunayen Yan Takarar Shugaban Kasa na Karshe gabanin Babban Zaben 2027
- Hukumar INEC na shirin sakin sunayen yan takarar shugaban kasa da mataimakansu gabanin babban zaben 2027
- INEC ta wallafa jerin wucin gadi na ‘yan takarar shugaban kasa 19 tare da wadanda za su tsaya musu takarar mataimakin shugaban kasa
- Sashe na 32(1) na Dokar Zabe ta 2026 ya tanadi cewa dole ne a fitar da jerin karshe na ‘yan takarar zabe akalla kwanaki 60 kafin ranar zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) za ta fitar da jerin karshe na ‘yan takarar da za su fafata a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da za a gudanar ranar 16 ga Janairu, 2027.
Ana sa ran hukumar za ta fitar da jerin sunayen a ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026.

Source: Facebook
INEC na shirin fitar da sunayen karshe
Majiyoyi sun shaidawa The Nation cewa jami’an hukumar na ci gaba da nazafi da kokarin kammala shirye-shiryen fitar jerin sunayen ‘yan takarar a Abuja.
Sashe na 32(1) na Dokar Zabe ta 2026 ya tanadi cewa dole ne a fitar da jerin karshe na ‘yan takarar zabe akalla kwanaki 60 kafin ranar gudanar da zaben.
INEC ta wallafa jerin wucin gadi na ‘yan takarar shugaban kasa 19 tare da wadanda za su tsaya musu takarar mataimakin shugaban kasa a watan da ya gabata.
Haka kuma hukumar ta fitar da jerin ‘yan takarar majalisar dattawa da na majalisar wakilai. Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasa a rana guda.
An rufe damar sauya ‘yan takara a zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasa ranar Asabar, 22 ga Agusta, yayin da aka rufe mika takardun tsayawa takara na Form EC 13A-E ranar Asabar, 29 ga Agusta, 2026.
Fitar da Form EC9 na ‘yan takara wani sharadi ne da Sashe na 29(3) na Dokar Zabe ta 2026 ta tanada, wanda ya wajabta wa INEC wallafa bayanan ‘yan takara bayan karbar takardunsu na tsayawa takara.
Sunayen wucin gadi da INEC ta saki
A cikin jerin sunayen wucin gadi na ‘yan takarar shugaban kasa d INEC ta fitar kwanakin baya akwai:
• Bola Tinubu – APC
• Atiku Abubakar – ADC
• Peter Obi – NDC
• Sanata Sandy Onor – PDP
• Omoyele Sowore – AAC
• Donald Duke – PRP
• Okwori Ada Elizabeth Frederick – NDP
• Chukwu Anita Zugwai – YPP
• Rufai Adekunle Omoaje – AA
• Adenuga Sunday – BP
• Memeh Samuel – DLA
• Nwanyanwu Daniel Danerechukwu – ZLP
• Okereke Sunday Chibuzor – LP
• Okereke Iken Esther – NRM
• Abbas-Bin Aliyu – ADP
• Dikwa Suleiman Mohammed – NNPP
• Adebayo Adewole Ebenezer – SDP
• Seyi Makinde – APM
• Yusuf Kabiru – APP
‘Yan takarar mataimakin shugaban kasa sun hada da:
• Kashim Shettima (APC)
• Rotimi Amaechi (ADC)

Kara karanta wannan
Alkali ya gargadi lauyoyi kan maganar shari’ar Atiku da Tinubu a Facebook da Twitter
• Rabiu Kwankwaso (NDC)
• Shehu Hussaini (AA)
• Egbeola Olawale Mertins (YPP)
• Ike Chinazam (ADP)
• Mustapha Usman Turaki (Boot Party)
• Balogun Alex (DLA)
• Chikwuemeka Uchenna Anthony (NDP)
• Magashi Haruna Garba (AAC)
• Umaru Babangida (PDP)
• Konto Hajja Bintu (LP)
• Hassan Khalid (ZLP)
• Samuel Magdalene Gali (NRM)
• Abubakar Isah (NNPP)
• Buba Musa (PRP)
• Bugaje Usman Mohammed (SDP)
• Ibrahim Adamu Bala (APM)
• Ofordile Peace Egobia (APP)

Source: Facebook
Duke ya nemi Najeriya ta canza tsari
A wani rahoton, kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya sake kira da Najeriya ta rungumi tsarin jam'iyyun siyasa biyu domin rage rudani.
Tsohon gwamnan jihar Cross River ya yi gargadin cewa karuwar gasar neman mulki na iya haifar da tashin hankali a fadin kasar tare da jefa Najeriya cikin babban rikici idan ba a dauki mataki ba.
Asali: Legit.ng

