2027: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi a Rushe Jam'iyyun Siyasa, a Bar Guda 2 a Najeriya

2027: Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Nemi a Rushe Jam'iyyun Siyasa, a Bar Guda 2 a Najeriya

  • Dan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya sake kira da Najeriya ta rungumi tsarin jam'iyyun siyasa biyu domin rage rudani
  • Duke ya yi gargadin cewa tsananin neman mulki na iya haifar da tashin hankali tare da jefa Najeriya cikin babban rikici
  • Tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, Justice Olukayode Ariwoola, ya bukaci 'yan takarar shugaban kasa su guji kalaman kiyayya da tunzura jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya sake kira da Najeriya ta rungumi tsarin jam'iyyun siyasa biyu domin daidaita fafatawar siyasa da rage rudanin da ke tattare da tsarin.

Duke ya yi wannan kira ne ranar Talata a Abuja lokacin da ya karbi bakuncin tawaga daga kungiyar Council of the Wise na Savannah Centre for Democracy, Diplomacy and Development (SCDDD).

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya fito ya fadi gaskiyar dalilin da ya sa yake neman mulkin Najeriya a 2027

Donald Duke.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PRP a zaben 2027, Donald Duke Hoto: Donald Duke
Source: Facebook

A rahoton Daily Trust, tsohon gwamnan jihar Cross River ya yi gargadin cewa karuwar gasar neman mulki na iya haifar da tashin hankali a fadin kasar tare da jefa Najeriya cikin babban rikici idan ba a dauki mataki ba.

Duke ya yi gargadi kan neman mulki

Duke ya ce yadda 'yan siyasa ke mayar da hankali wajen neman mulki ko ta halin kaka ya raunana muhimman dabi'un dimokuradiyya.

A cewarsa, siyasa a Najeriya ta sauya daga wata hanya ta yi wa jama'a hidima zuwa wani fanni na neman mulki cikin tsananin gaggawa.

Tsohon gwamnan ya ce akwai bukatar a sake duba tsarin siyasar kasar domin rage rikice-rikice da kuma tabbatar da cewa fafatawar siyasa ba ta zama barazana ga zaman lafiyar kasa ba.

Tsohon alkalin alkalai ya yi gargadi

Tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya, Justice Olukayode Ariwoola, ne ya jagoranci tawagar kungiyar da ta ziyarci Duke.

Kara karanta wannan

Yadda ake ciki a kasar Nijar da sojoji suka yi yunkurin yi wa Tchian juyin mulki

Ziyarar na daga cikin kokarin kungiyar na tattaunawa da manyan jagororin siyasa domin inganta zaman lafiya yayin gudanar da yakin neman zabe gabanin zaben 2027.

Ariwoola ya bukaci dukkan 'yan takarar shugaban kasa su tabbatar da cewa yakin neman zabensu ya kasance ba tare da kalaman kiyayya, kalamai masu tunzura jama'a ko kira zuwa tashin hankali ba.

Ariwoola
Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya (CJN), Olukayode Ariwoola Hoto: @NGRPresidency
Source: UGC

Tunawa da rikicin zaben 2011

Tsohon Alkalin Alkalai ya yi nuni da mummunan tarihin rikice-rikicen da suka biyo bayan zabuka a Najeriya, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Ya tunatar da yadda tashin hankalin da ya biyo bayan babban zaben shekarar 2011 ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 1,000, musamman a jihohin Arewacin Najeriya.

Ariwoola ya soki yadda wasu 'yan siyasa ke daukar zabe a matsayin batun “rayuwa ko mutuwa”, inda ake amfani da 'yan daba, sayen kuri'u, magudin zabe da cika akwatin zabe ba bisa ka'ida ba.

Dalilin Donald Duke na neman takara

A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na PRP, Donald Duke, ya ce ya shiga takara ne domin magance matsalolin Najeriya tare da inganta rayuwar 'yan kasa.

Ya ce duk da cewa shugabannin da suka jagoranci Najeriya tun 1979 sun zo da manufofin siyasa, babu wanda ya zo da cikakkiyar manufar shugabanci da za ta samar wa kasar ci gaba da sauyin tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262