Shirin Cire Tinubu a Mulki: Jam'iyyarPDP Ta Fadi Matsayarta kan Hadaka a 2027
- Jam'iyyar PDP ta amince da shirin G-100 na hada jam’iyyun adawa domin samar da tsayayyen dan takara da zai kalubalanci APC
- PDP ta ce shiga wannan tafiya ya dogara ne kan gaskiya, daidaito, amfani da bayanai wajen yanke hukunci da samar da tsarin siyasa mai adalci
- Ta bayyana cewa hadin kan ‘yan adawa zai taimaka wajen kwace mulki daga APC da sake gina Najeriya tare da magance talauci da rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - A yayin da zaben shugaban kasa na 2027 ke karatowa, PDP karkashin jagorancin Tanimu Turaki ta amince da shirin G-100 na hada ‘yan adawa wuri guda.
G-100 kungiya ce da ta kunshi manyan jiga-jigan jam’iyyun adawa 100, wadanda ke kokarin samar da wata babbar kawance domin kalubalantar Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Atiku ko Obi: Yan adawa sun fara ɗaukar matsayan da za ta iya kayar da Tinubu a zaben 2027

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da PDP ta fitar a ranar Talata 1 ga watan Satumbar 2026 wanda ta wallafa a shafin X.
PDP ta shiga hadakar jam'iyyun adawa
Kwamred Ini Ememobong, Sakataren Yada Labarai na Kasa na PDP, ya bayyana goyon bayan jam’iyyar ga wannan mataki.
Ememobong ya yaba da ra’ayin kungiyar na samar da dan takara guda daya da zai wakilci ‘yan adawa.
Ya ce PDP ta shiga shirin ne bisa alkawarin cewa za a gudanar da tsarin cikin gaskiya, daidaito da kuma bai wa kowane bangare dama.
Sanarwar ta ce:
“Wannan shawara ta samo asali ne daga korafin yan Najeriya da ke fama da matsin lamba a karkashin gwamnatin tarayya ta Bola Tinubu da APC.”
Ta kara da cewa akwai bukatar jam’iyyun siyasa masu nagarta su hada karfi domin ceto kasar daga matsalolin da ke addabarta.

Source: UGC
Abin da Tanimu Turaki ya ce
Turaki ya ce irin wannan shugabanci zai taimaka wajen rage tsananin talauci da kuma matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a kasar.
A cewar Shugaban PDP na Kasa, Kabiru Tanimu Turaki SAN:
“Shigarmu cikin wannan tsari ya dogara ne kan alkawarin cewa za a gudanar da shi bisa gaskiya, daidaito, amfani da bayanai wajen yanke hukunci da adalci.”
Ya ce duk wani sakamako da aka samu daga tsarin da aka gina kan wadannan ka’idoji zai iya samar wa ‘yan Najeriya ingantaccen shugabanci.
Ya kara da cewa:
"Wannan mataki ya yi daidai da matsayinmu na baya na yin aiki da jam’iyyun siyasa da kungiyoyin da suke son ceto kasar daga matsalolin da gwamnatin APC ta haifar.”
PDP ta ce halartar taron farko na kungiyar G-100 da aka gudanar a ranar 31 ga Agusta, 2026, ya kara nuna shirinta na bayar da gudunmawa wajen kafa kawancen ‘yan adawa.
An rasa Atiku, Obi da Kwankwaso a taron hadaka
An ji cewa taron gamayyar jam’iyyun adawa da aka shirya domin 2027 ya gamu da cikas, bayan Atiku, Obi, Kwankwaso da Amaechi sun kasa halarta.
Jam’iyyun adawa da suka halarta sun amince da kafa tsarin haɗin gwiwa domin samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda a zaɓen 2027.
Masu shirya taron sun yi gargaɗin cewa rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan adawa na iya bai wa APC damar samun nasara a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

