Za a Yi Zaɓen Fitar da Gwani domin Sauya Ɗan Takarar Gwamna a Gombe, Nasarawa
- Jam’iyyar SDP ta sanar da INEC cewa za ta gudanar da sabon zaben fitar da gwani na gwamna a Gombe da Nasarawa
- SDP ta ce za a gudanar da zabukan ne ta hanyar zaben fitar da gwani kai tsaye, a yau Asabar da karfe 11 na safe a jihohin biyu
- A Gombe, za a gudanar da zaben a sakatariyar SDP ta jihar, yayin da za a gudanar da na Nasarawa a Ta’al Hotel da ke Lafia
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar SDP ta sanar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) cewa za ta gudanar da sabon zaben fitar da gwani na gwamna a Gombe da Nasarawa
Matakin ya biyo bayan janyewar ’yan takarar da jam’iyyar ta tsayar a matsayin ’yan takararta na gwamna a jihohin biyu, lamarin da ya sa ake bukatar maye gurbinsu.

Source: Twitter
SDP ta tura wa INEC sako
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata wasika mai kwanan wata 24 ga Agusta, 2026, wadda aka aika wa shugaban INEC, inda ta ce za a yi zaben ta hanyar zaben fidda gwani kai tsaye, cewar Punch.
A cewar sanarwar da shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Sadiq Gombe, da sakataren kasa, Dakta Olu Agunloye, suka sanya wa hannu, za a gudanar da zabukan ne a yau Asabar da karfe 11 na safe.
Sanarwar mai taken, “Sanarwar Zaben Fidda Gwani na Jam’iyya Domin Maye Gurbin ’Yan Takarar Gwamna na Social Democratic Party,” ta ce jam’iyyar ta gayyaci hukumar INEC domin sanya ido kan zaben.
Jam’iyyar SDP ta ce za a gudanar da zabukan ne domin maye gurbin ’yan takarar gwamna da suka janye daga takarar, ta hanyar tsarin zaben fidda gwani kai tsaye.

Source: Original
Yadda aka tsara gudanar da zaɓen
A Gombe, za a gudanar da zaben fidda gwani a Sakatariyar jam'iyyar SDP ta Jihar Gombe, yayin da a Nasarawa za a gudanar da shi a Ta’al Hotel da ke Lafia.
Sanarwar ta ce:
"Muna son sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), tare da gayyatar ta domin ta sanya ido kan zaɓen fitar da gwani na maye gurbin ’yan takarar gwamna, sakamakon janyewar ’yan takarar da aka zaɓa daga tseren.
"A Gombe, za a gudanar da zaɓen ne a Sakatariyar Jam’iyyar ta Jiha da ke Gombe, a Nasarawa, za a gudanar da zaɓen fitar da gwani a Ta’al Hotel, Ladia, babban birnin jihar."
Sanarwar ta kuma kunshi takardun da ’yan takarar da suka yi murabus suka gabatar, ciki har da wasikun janyewa da takardun rantsuwar da suka tabbatar da matakin nasu, cewar Daily Post.
Sabon tsarin SDP kan zaben 2027 a Najeriya
A baya, kun ji cewa jam'iyyar SDP mai adawa ta bayyana cewa ga dukkan alamu ita za ta lashe zaɓen shugaban kasa mai zuwa a shekarar 2027.
Mataimakin shugaban SDP na Arewa ta Tsakiya, Abubakar Dogara ya ce idan Allah ya yarda za su kwace mulki daga hannun Bola Tinubu.
Dogara ya yi kira ga ƴan Najeriya da su marawa SDP baya kuma su yi rijistar zama cikakkun ƴan jam'iyya a mazaɓunsu.
Asali: Legit.ng

