Alkali Ya Gargadi Lauyoyi kan Maganar Shari’ar Atiku da Tinubu a Facebook da Twitter
- Atiku Abubakar da jam'iyyar ADC na kalubalantar takarar Bola Tinubu, ana zarginsa da mika takardar bogin shaidar NYSC
- Alkali ya yi gargadi cewa kotu ita ce kadai wurin gudanar da shari'a, ba shafukan sada zumunta ko kafafen watsa labarai ba
- Bayan jan kunnen lauyoyi da ya yi, Inyang Ekwo ya ce kotu ta dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Satumba 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Inyang Ekwo shi ne yake sauraron karar da Atiku Abubakar ya shigar domin a hana Bola Ahmed Tinubu sake takara.
Lauyoyin Atiku Abubakar sun je kotun tarayya a Abuja, suna so a haramta wa Bola Tinubu sake neman takara a zaben 2027.

Source: Getty Images
NYSC: Shari'ar Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Ana shari’a ne a kan zargin shugaban Najeriya da mika wa INEC takardar kammala bautar kasa na karya in ji jaridar The Cable.

Kara karanta wannan
Lauya ya jawo matsala a karar da Atiku ya kai kotu kan takarar Tinubu a zaben 2027
Yayin da ake kokarin sauraron karar, Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi wa lauyoyi gargadi game da tattauna mas’alar saboda yanayinta.
Ekwo ya ce a zauren kotu za a rika shari’ar ba a fita waje a yi ta surutu a kafafen sada zumunta na zamani ko gaban ‘yan jarida ba.
Kashedin da alkali ya yi wa lauyoyi
Mai shari'an ya ce idan kotu ta samu lauyoyi sun saki baki kan shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026, za su yaba wa aya zakinta.
Alkalin ya yi magana da kaukasan harshe, yana mai cewa idan aka saba wa umarnin da ya bada, zai dauki mataki mai tsauri a kotu.
"Za a yi wannan shari’a ne a kotu ba a kafafen yada labarai ba, ko gama-garin kafofi ne ko shafukan sada zumunta.
"Idan aka tattauna shari’ar nan a shafukan sada zumunta na zamani, zan kama lauyan bangaren da laifi kuma zan dauki mataki mai tsauri sosai."
- Alkali Inyang Ekwo
Vanguard ta rahoto alkalin yana bukatar masu kara su gabatar da hujjojinsu game da badakalar ta NYSC gaban kotun tarayyar.
Lauyoyin Atiku, Tinubu da INEC sun hallara a kotu
A zaman da aka yi ranar Talata, an ji yadda Omosanya Popoola ya wakilci shugaban Najeriya a matsayin lauya mai ba shi kariya.
Lokacin ne lauyan Atiku Abubakar wato Joseph Onu ya fada wa kotu cewa ba su iya aika wa Bola Tinubu da takardun shari’ar ba.
Lauyan da ya shigar da kara yana so a ankarar da shugaban kasar game da shari’ar tun farko saboda gudun a samu matsala nan gaba.
Wanda yake tsaya wa INEC a kotun shi ne Alex Iziyon. Kuma bayan zaman da aka soma, an daga karar zuwa 28 ga Satumba 2026.

Source: Getty Images
Tinubu zai yi aiki duk da yana hutu
An samu karin bayanin abin da ya hana Bola Tinubu ya ba Kashim Shettima rikon mulki duk da zai shafe kwanaki bai Najeriya.
Ko da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafi hutu a Ingila, fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa har a can ma aiki zai rika yi.
Sunday Dare ya yi wannan bayani gabanin jirgin shugaban Najeriyan ya tashi a Abuja, ya ce za a rika karbar rahoto daga Turai.
Asali: Legit.ng

