Hukumar INEC za Ta Yi Zaben Shugaban Kasa na Gwaji a 2027

Hukumar INEC za Ta Yi Zaben Shugaban Kasa na Gwaji a 2027

  • INEC na shirin gudanar da gwajin zaben shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen 2027 domin duba yadda tsarin tantance masu zaɓe zai gudana
  • Gwajin zai kuma taimaka wajen tabbatar da ingancin aika sakamakon zaɓe da kuma yadda jama'a za su iya kallon sakamakon zaɓe da za a yi
  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya ce ya zama dole tabbatar da sahihancin zaɓen 2027 wajen yaki barazanar yaɗuwar bayanan ƙarya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) na duba yiwuwar gudanar da gwajin zaben shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja yayin taron shekara-shekara na 13 na Ƙungiyar Masana Sadarwa ta Najeriya (ACSPN).

Kara karanta wannan

INEC ta fadi abin da ake tsoro ya hana zaben 2027 zama sahihi

Shugaban INEC, Farfesa Amupitan
Farfesa Joash Amupitan a hadu da masu kada kuri'a a dama. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Dailu Trust ta wallafa cewa an gabatar da jawabin nasa ne ta hannun kwamishinan INEC, Sani Adam, a taron da aka gudanar a Abuja.

INEC za ta yi zaben gwaji

Amupitan ya ce gwajin zaben da ake shirin gudanarwa zai taimaka wajen gwada tsarin tantance masu zaɓe, aika sakamakon zaɓe da kuma kallon sakamakon a yanayi mai kama da ranar zaɓe ta gaske.

Punch ta wallafa cewa ya ce shirin na daga cikin matakan da hukumar ke ɗauka domin tabbatar da cewa fasahar da za a yi amfani da ita a zaɓen 2027 tana aiki yadda ya kamata.

Shugaban INEC ya kuma ce hukumar na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da cikakken bincike kan tsarin fasahar zaɓe, yayin da shirye-shiryen gwajin zaben ke tafiya tare da tsarin kasafin kuɗin zaɓen.

Hadin gwiwa da masana sadarwa

Shugaban INEC ya gayyaci ACSPN da sauran masana sadarwa da su kafa tsarin haɗin gwiwa da hukumar wajen gudanar da bincike kan ilimin kafofin yaɗa labarai, gano abubuwan da AI ta ƙirƙira da kuma horas da 'yan jarida.

Kara karanta wannan

'Dole ku kawo yankunanku ga APC': Gwamna ya yi barazana ga ciyamomi

Ya ce masu zaɓen 2027 za su fi kasancewa matasa kuma za su dogara sosai da fasahar wayar hannu fiye INEc al'ummomin baya, inda wayoyin zamani za su iya zama babbar hanyar samun bayanan da suka shafi zaɓe.

Yadda aka yi zaben Ondo
'Yan NYSC a wajen zaben Ondo. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Sai dai ya yi gargaɗin cewa bai kamata Najeriya ta kwafi hanyoyin fasahar zaɓe na wasu ƙasashe kai tsaye ba, domin dole ne a daidaita su da yanayin ƙasar.

INEC ta gargadi jama'a

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar INEC ta gargadi 'yan Najeriya kan wata sanarwar bogi da ke yaɗuwa a intanet, wadda ke ikirarin cewa hukumar ta fara daukar ma'aikatan wucin gadi.

INEC ta ce saƙon da ake yaɗawa yana umartar masu neman aikin da su shiga wani shafin intanet da ake ikirarin an ƙirƙira domin gudanar da aikin daukar ma'aikatan.

Hukumar ta jaddada cewa sanarwar ba ta fito daga gare ta ba, tana mai kira ga jama'a da su yi hattara da irin waɗannan bayanai da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng