Jita jitar Opay da Shahararrun Labaran Bogi da Suka Rika Yawo Makon Jiya a Najeriya

Jita jitar Opay da Shahararrun Labaran Bogi da Suka Rika Yawo Makon Jiya a Najeriya

Nigeria - Labaran karya suna nema su zama ruwan dare musamman shafukan sada zumunta ba a Najeriya kadai ba har da kasashen waje.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

A cikin ‘yan kwanakin nan, mun ci karo da wasu labarai da yawa wadanda kirkirar su aka yi ko kuma an yi masu wata fahimta can ta dabam.

Sanusi II
Hafsoshin tsaro a Najeriya, hoton wani sakon karya da sunan Opay da Sarki Muhammadu Sanusi II
Source: Getty Images

Dama can kafar Facebook ta yi kaurin suna wajen tattaro labarai marasa inganci. Wannan matsala ta karu sosai tunda aka kirkiro fasahar AI.

Dandalin X da ya fi shahara da Twitter cike yake da labaran karya na kalamai da aka kikira musamman idan aka shiga fagen kwallon kafa.

Labaran karya da suka yi ta yawo

Legit Hausa ta kawo wasu daga cikin manyan labaran bogin da ta ci karo da su:

1. Opay za su je hutu

Kara karanta wannan

Da gaske hukumar Hisbah ta hana Kiristoci gudanar da ibada a Sokoto

Kwatsam aka ga mutane daga ciki har da matashin ‘dan siyasar nan, Adamu Garba II suna yada labari a Facebook cewa Opay za su tafi hutu.

Labarin karyar da aka gani ya yi ikirarin daga 1 ga Satumba 2026 kamfanin zai je hutun sai baba-ga-gani kuma mutane su yi sauri su cire kudinsu.

Kamfanin ya yi maza ya karyata zancen a dandalin X da shafin yanar gizo. Tuni an ba shi shawarar ya yi shari’a a kotu da masu yada sharrin.

2. Soke kwamitin yakin zaben APC

Wasu sun fito suna cewa fadar shugaban kasa ta soke kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu/Kashim Shettima da aka fitar a makon jiya.

Jaridar The Cable ta rahoto Felix Morka yana cewa labarin karya ne, yake cewa maganar soke sunayen ‘yan kamfen da aka fitar jita-jita ce.

Sai dai Kakakin na APC ya ce idan akwai bukatar a sabunta jerin, za a yi hakan. Wannan ya yi daidai da abin da jaridar Legit Hausa ta rahoto.

3. Hafsun tsaro ya yi wa Tinubu mubaya’a

Kara karanta wannan

Ribadu, Dikko Radda da mutum 10 da Tinubu ya manta da su a kwamitin yakin zabe

Har bidiyo aka kirkira domin nuna cewa Janar Olufemi Oluyede ya tsoma kan shi a siyasa, yana goyon bayan tazarcen Bola Tinubu a 2027.

Da jin bullar bidiyon karyar, Hedikwatar tsaro ta fitar da jawabi domin karyata zancen, ta ce sharri aka yi wa Hafsun tsaro ta hanyar fasahar AI.

Jawabin ya ce jami’an tsaro suna aikinsu bisa ka’ida ba tare da nuna bangarancin siyasa ba, za a samu labarin karyatarwar a jaridar PM News.

4. Buratai ya ce Tinubu zai kunyata Najeriya?

Yanzu haka ana shari’a a Amurka inda wasu suka bukaci a fito da bayanan shari’ar zargin harkar kwayoyi da aka taba yi da Bola Tinubu.

Wasu ma’abota WhatsApp sun rika yawo da wani hoto mai dauke da cewa Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce fitar da bayanan zai kunyata Najeriya.

An yi ikirarin tsohon hafsun sojojin kasar ya fadi wannan. Binciken Legit Hausa ya nuna an juya maganar da tsohon jakadan na Benin ya yi.

Leadership ta rahoto Buratai ya ce abin da ya faru shekaru 33 a Amurka ya wuce, kuma tado maganar za ta iya taba martabar kasar da jama'anta.

Kara karanta wannan

Bill Gates ya fadi hadarin AI zai haifar a duniya a shekaru masu zuwa

5. Sanusi II ya yi wa raddi?

Akwai masu yada cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi kaca-kaca da Atiku Abubakar saboda ya yi zancen maido tallafin man fetur.

Wani masoyin Bola Tinubu, Mista Abdullah Ayofe ya daura tsohon bidiyon Sarkin Kano a X lokacin yake magana game da zaben 2023.

Sanusi II ya fada wa masu takaran da ta wuce su shirya daukar matakai masu wahala, ba martani yake maida wa ‘dan takaran ADC a 2027 ba.

Badakalar hukumar bogi cikin gwamnati

Rahoto ya zo cewa Gwamnatin Tarayya ta dakatar da wata hukumar bogi, kafin nan tana shirye-shiryen kiran taron da zai kawo wa Najeriya ₦50bn.

Tun a lokacin Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin gaggauta kamawa da bincikar shugaban wannan hukuma ta karya, George Buchi Nwabueze.

Ita Gwamnatin tarayya ta musanta sanin zaman hukumar ko labarin gudanar da irin wannan harkar da hadin kan Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya,

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng