Dama ga Matasa: Za a Dauki Yan Soshiyal Midiya 4000 domin Tallata Bola Tinubu

Dama ga Matasa: Za a Dauki Yan Soshiyal Midiya 4000 domin Tallata Bola Tinubu

  • Gwamnatin Tarayya ta shirya ɗaukar yan soshiyal midiya 4,000 msu karfin mabiya a kafafen sada zumunta domin tallata ayyukan Shugaba Tinubu
  • Ministan Ayyuka, David Umahi ya ce za a yi amfani da yan midiya wajen isarwa da bayanan ayyukan gwamnati ga ’yan Najeriya, musamman matasa
  • Ya ce aikin kwalta na kilomita 105 na hanyar Lagos-Calabar zai kammala nan da watan Nuwamba, 2026.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin ɗaukar yan soshiyal midiya 4,000 da ke da tasiri a kafafen sada zumunta domin nuna ayyukan more rayuwa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gudanar.

Ministan Ayyuka, David Umahi, ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja yayin da yake karɓar rahoton da Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS) ta gabatar kan duba ayyukan hanyoyin gwamnatin tarayya a Kano, Jigawa, Kaduna da Sokoto.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hango abin da ba zai wa 'yan Najeriya daɗi ba kan dawo da tallafin fetur

Umahi.
Ministan ayyuka na tarayya, Dave Umahi tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: David Umahi
Source: Twitter

Za a dauki yan soshiyal midiya 4000

A rahoton The Cable, Umahi ya ce sabuwar hanyar amfani da yan midiya za ta taimaka wajen isar da bayanan ayyukan gwamnati kai tsaye ga ’yan Najeriya, musamman matasa, yayin da zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa.

“Dole ne mu fuskanci wannan yaƙin na kafafen sada zumunta. Dole mu dauki yan soshiyal midiya 4,000 domin su bayyana abubuwan da muke yi a kafafen sada zumunta,” inji shi.

Ministan ya ce ya kamata ’yan Najeriya su samu bayanai kan abubuwan da gwamnatin Tinubu ta cimma.

Ya kuma ce gwamnati za ta yi la’akari da gina gadojin masu tafiya a ƙafa a kusa da harabar jami’o’i bayan NANS ta nuna damuwa kan hakan yayin ziyarar duba ayyukan.

Umahi ya yaba wa ƙungiyar ɗaliban saboda gudanar da bincike da kanta kan ayyukan gwamnati da kuma tantance tasirinsu ga jama’a.

Yaushe za a kammala titin Lagos-Calabar?

Kara karanta wannan

An hada mata musulmai da Allah SWT kan sake zaben Tinubu da Shettima a 2027

Ministan ya kuma ce aikin shimfiɗa kwalta na kilomita 105 da ake yi a kan babbar hanyar Lagos-Calabar zai kammala nan da watan Nuwamba.

Ya kuma nuna damuwa kan lalata kayan aikin da ake yi a gefen hanyar, yana mai cewa wasu mutane na lalata kayayyakin more rayuwa tare da cire na’urorin tsaro da aka girka.

Hanyar Lagos-Calabar ta kasance cikin ce-ce-ku-ce kan nazarin tasirin aikin ga muhalli (EIA), tsarin da aka bi wajen shimfiɗa hanyar da kuma yiwuwar tasirinta kan ambaliyar ruwa a Legas.

Umahi.
Ministan ayyuka kuma tsohon gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi Hoto: David Umahi
Source: Twitter

Umahi ya ce an tsara hanyar ne ta yadda za ta taimaka wajen rage ambaliyar ruwa, yana mai cewa an haɗa tsarin magudanan ruwa cikin aikin domin fitar da ruwa daga yankunan da ke kewaye.

Wani matashi dan midiya, Abdul Dabai ya shaidawa Legit Hausa cewa wannana matakin ba zai canza tunanin mutane kan zaben 2027 ba.

Matashin ya ce talakawa sun zo wuya, da yawan yan Najeriya hakurinsu ya kare kan wahalhalun da aka shiga tun bayan hawan Bola Tinubu.

"Yan soshiyal midiya ba za su iya ceto wannan gwamnati daga fushin talakawa ba, saboda mutane sun gaji, ana ta cewa su yi hakuri sauki na tafe amma har yanzu shiru," in ji shi.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 7 sun shilla ƙasar Amurka, sun nemo abin da zai amfani 'yan Najeriya

Tinubu ya tsawaita hutun da ya tafi

Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai dawo Najeriya a ƙarshen mako bayan ya ƙara tsawaita hutunsa da wasu ‘yan kwanaki.

Idan baku manta ba, Shugaba Tinubu ya bar Najeriya ranar 30 ga Agusta zuwa London domin fara hutu, inda daga bisani ya wuce kasar Faransa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262