Me Zai Faru idan Aka Kayar da APC a Zabe karkashin Mulkin Tinubu? Gwamna Ya Yi Bayani

Me Zai Faru idan Aka Kayar da APC a Zabe karkashin Mulkin Tinubu? Gwamna Ya Yi Bayani

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce mulkin Bola Tinubu ya tabbatar cewa jam'iyya mai mulki na iya faduwa zabe ba tare da wata matsala ba
  • Ya yi nuni da zaben gwamnan Osun da Ademola Adeleke ya lashe a matsayin hujjar jajircewar Tinubu wajen kare dimokuradiyya
  • Sanwo-Olu ya jaddada cewa tsarin zaben Najeriya ya inganta fiye da baya, ya kuma yi kira ga INEC ta shirya tsaf kafin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya bayyana a matsayin jajircewarsa wajen tabbatar da ka'idojin dimokuradiyya a Najeriya.

Sanwo-Olu ya ce a karkashin mulkin Tinubu, jam'iyya mai mulki, APC na iya faduwa zabe a wata jiha kuma babu abin da za a iya yi.

Kara karanta wannan

2027: Shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ya samu gagarumar goyon baya

Gwamnan Legas.
Gwamnan jihar Legas, babajide Sanwo-Olu a ofishinsa da ke gidan gwamnati Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Source: Getty Images

Jaridar The Cable ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana haka ne ranar Alhamis yayin lakcar shekara-shekara ta bakwai da Freedom Online ta shirya a Sheraton Hotel da ke Ikeja a jihar Legas.

Sanwo-Olu ya yi magana kan zaben Osun

Gwamna Sanwo-Olu ya yi nuni da zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar 15 ga watan Agusta, wanda gwamna mai ci, Ademola Adeleke, ya lashe.

Adeleke na jam'iyyar Accord ya kayar da Bola Oyebamiji na jam'iyyar APC da tazarar kuri'u sama da 60,000.

Bayan zaben, Shugaba Tinubu ya taya Adeleke murnar sake lashe zaben, yana mai bayyana nasarar a matsayin wata tabbaci cewa dimokuradiyya za ta ci gaba da bunkasa a karkashin gwamnatinsa.

"APC za ta iya faduwa zabe a mulkin Tinubu"

Sanwo-Olu ya ce abin da ya faru a Osun ya bambanta da yadda siyasar Najeriya ta kasance a baya, lokacin da jam'iyyun adawa ke fuskantar matsala wajen samun nasara a kan jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa gwamnoni umarni su inganta rayuwar talaka

Ya ce:

“Akwai wani lokaci a wannan kasa da kalmar ‘ikon gwamnatin tarayya’ ta kasance wani abu da jam'iyya mai mulki ke amfani da shi ba tare da wata kunya ba.
“A karkashin wannan shugaban kasa, jam'iyya mai mulki na iya faduwa zabe a wata jiha a Kudu maso Yamma, amma ba abin da ya faru, sama ba ta fado ba. Wannan shi ne yadda dimokuradiyya take.”

Gwamnan jihar Legas ya ce Tinubu mutum ne da ya dade yana fafutukar tabbatar fa bin tsarin dimokuradiyya.

Sanwo-Olu ya bukaci INEC ta shirya

Sanwo-Olu ya ce tsarin gudanar da zabe a Najeriya ya samu ci gaba sosai, inda ya ambaci dokar zabe ta 2022, sabuwar dokar zabe ta 2026 da kuma amfani da fasaha wajen tantance masu kada kuri'a da tura sakamakon zabe.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubua a wurin taron tattalin arziki na duniya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Sai dai ya ce akwai sauran aiki domin tabbatar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shirya tsaf domin babban zaben 2027, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An lissafa biliyoyin da Tinubu da Remi suka kashe a tafiye tafiyen shekaru 3

Ya ce:

“Dole ne INEC ta kasance a shirye a kowace rumfar zabe ranar 16 ga Janairu da kuma ranar 6 ga Fabrairu, kuma kowannenmu yana da alhakin taimaka mata wajen yin shiri.”

Gwamnan Osun zai koma APC?

Kun ji cewa Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Imole ya yi martani game da rahotannin da ke cewa Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, na shirin ficewa daga jam'iyyar Accord zuwa APC.

Kwamitin ya ce ziyarar da Adeleke ya kai wa Shugaba Bola Tinubu al’ada ce bayan zaɓen gwamna da aka kammala, amma ba ta da alaƙa da shirin sauya jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262