Gwamnan APC Ya Tona Gaskiya, An Ji Yadda Gwamnoni Suka Amfana da Cire Tallafin Fetur
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce jihohi da kananan hukumomi sun samu karin kudaden shiga bayan cire tallafin man fetur
- Ya ce yanzu ya rage ga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi su yi amfani da kudaden yadda ya kamata don inganta rayuwar al'umma
- Gwamna Sanwo-Olu ya ce masu kada kuri'a za su tantance ayyukan gwamnati kafin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ce jihohi da kananan hukumomi a fadin Najeriya sun amfana matuka sakamakon cire tallafin man fetur a karkashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sanwo-Olu ya bayyana haka ne a wajen lakcar shekara-shekara ta bakwai da Freedom Online ta shirya mai taken, “Zaben 2027: Tattalin Arziki, Tsaro da Makomar Najeriya.”

Source: Getty Images
A rahoton Daily Trust, gwamnan ya ce karin kudaden da jihohi da kananan hukumomi ke samu bayan cire tallafin ya ba su damar samun karin kudaden gudanar da ayyukan ci gaba da inganta rayuwar jama'a.

Kara karanta wannan
Me zai faru idan aka kayar da APC a zaɓe karkashin mulkin Tinubu? Gwamna ya yi bayani
Sanwo-Olu ya yi magana kan karin kudi
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta taka nata rawar wajen tabbatar da cewa karin kudade sun shiga hannun jihohi.
Sai dai ya ce alhakin yadda za a yi amfani da kudaden yanzu ya rataya ne a wuyan gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi.
Sanwo-Olu ya ce:
“A karkashin wannan shugaban kasa, jihohi sun amfana sosai. Tun bayan cire tallafin mai, kudaden da ake rabawa jihohi da kananan hukumomi sun karu matuka.
“Shugaban kasa ya yi nasa bangaren; kudin suna zuwa. Abin da za a yi da su ya rage gare mu. An cire duk wani uzuri, kuma masu kada kuri'a sun fi fahimtar abin da ke faruwa.”
Abin da mutane za su duba kafin zabe
Gwamnan Legas ya ce ba lallai ba ne 'yan Najeriya su kasance masana tattalin arziki kafin su iya tantance ayyukan gwamnati, cewar rahoton Vanguard.
Ya ce jama'a sun zama kamar kwararrun masu lissafin yadda gwamnati ke kashe kudaden jama'a, saboda suna iya ganin tasirin kashe kudaden a rayuwarsu ta yau da kullum.

Source: Facebook
Sanwo-Olu ya ce masu kada kuri'a za su tantance ayyukan gwamnatoci a fannoni kamar samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya da sauran muhimman ayyuka yayin da za su je rumfunan zabe a 2027.
Ya bukaci gwamnatocin jihohi su yi amfani da karin kudaden da suke samu yadda ya kamata tare da nuna wa jama'a gaskiya da rikon amana.
APC na iya faduwa zabe a mulkin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ce mulkin Bola Tinubu ya tabbatar cewa jam'iyya mai mulki na iya faduwa zabe ba tare da wata matsala ba.
Gwamna Sanwo-Olu ya yi nuni da zaben gwamnan jihar Osun da aka gudanar ranar 15 ga watan Agusta, wanda gwamna mai ci, Ademola Adeleke, ya lashe.
Ya ce abin da ya faru a Osun ya bambanta da yadda siyasar Najeriya ta kasance a baya, lokacin da jam'iyyun adawa ke fuskantar matsala wajen samun nasara a kan jam'iyya mai mulki.
Asali: Legit.ng
