Kotun Musulunci Ta Dauki Matakin Farko kan Wadanda Ake Zargi da Kisan Dan Shagamu a Kano

Kotun Musulunci Ta Dauki Matakin Farko kan Wadanda Ake Zargi da Kisan Dan Shagamu a Kano

  • Kotun Shari’a ta Kofar Kudu ta bayar da umarnin tsare mutane uku kan zargin haɗa baki wajen kashe Ibrahim Khalil Dan Shagamu
  • Ana zargin mutanen sun shiga gidan fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa da ke Kumbotso a Kano da daddare tare da yanke masa maƙogaro
  • Bayan zaman sauraron shari'ar, lotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa 17 ga watan Nuwamba, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a jihar Kano ta fara sauraron karar da aka dhigar gabatanta kan kisan fitaccen mai sharhi a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalid Dan shagamu.

Yayin wannan zama, kotun ta bayar da umarnin tsare mutane uku a gidan gyaran hali kan zargin haɗa baki wajen kashe Dan Shagamu.

Dan Shagamu.
Fitaccen mai sharhi a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu Hoto: Ibrahim Khalil Dan Shagamu
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotu ta dauki wannan matakin ne bayan gurfanar d wadanda ake zargi da akkata kisan.

Kara karanta wannan

2027: Bayan hukuncin kotu, PDP ta ɗauki matsaya kan takarar Sheikh Pantami a jihar Gombe

An gurfanar da wadanda ke zargi da kisa

Rundunar ’yan sanda ta gurfanar da mutanen ukun a gaban kotun bisa zargin haɗa baki da kisan kai. Sunayen wadanda ake tuhumar su ne Aliyu Adamu, Salihu Haruna da Sani Muhammad.

Kotun Shari’a ta Kofar Kudu, wadda Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ke jagoranta, ta umarci a tsare Aliyu Adamu, Salihu Haruna da Sani Muhammad har zuwa ranar 17 ga Nuwamba, 2026.

Ana zargin waɗanda ake tuhumar da kutsa kai gidan Ibrahim Khalil Dan Shagamu da ke Unguwar Gaida, a ƙaramar hukumar Kumbotso ta Kano, da misalin ƙarfe 11 na dare ranar 8 ga Satumba, 2026.

Ana zargin cewa bayan sun shiga gidan, sun kashe shi ta hanyar yanke masa maƙogaro, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Mutanen da ake zargi sun musanta

Sai dai bayan karanto masu duka tuhume-tuhumen da ake masu, mutane uku da ake zargi sun musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake yi musu.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 61, an ceto shugaban ƙaramar hukumar da ya fada tarkon yan bindiga

Bayan sauraron ƙarar, kotun ta bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali, sannan ta ɗage shari’ar zuwa ranar 17 ga Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a zaman kotu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kisan gillan da aka yi wa Dan Shagamu ya tada kura a Najeriya musamman a jihar Kano, inda manyan shugabanni da yan takara suka nemi a gudanar da bincike.

Tun bayan aukuwar lamarin, rundunar yan sandan Kano ta sanar da kama mutum uku bisa zargin hannu a kashe Dan Shagamu, kuma a yanzu an gyrfanar da su gaban kotu.

'Ya'yan Dan Shagamu sun nemi adalci

A wani labarin, kun ji cewa babban ɗan marigayi Ibrahim Khalil Dan Shagamu, Ammar Ibrahim Dan Shagamu, ya buƙaci a yi wa mahaifinsa adalci.

Ammar ya bayyana mutuwar mahaifinsa a matsayin babban rashi mai raɗaɗi, yana cewa shi da ’yan uwansa biyar har yanzu suna fama da jimamin abin da ya faru.

Ya ce ya bar gida kimanin shekaru huɗu da suka gabata, kafin a kira shi ba zato ba tsammani da labarin kisan mahaifinsa cikin mummunan yanayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262