Barayin Waya Sun Shiga Gida Sun Kashe Uwa Mai Yara 5 da Wuka a Gombe
- An kashe wata mata mai ’ya’ya biyar bayan wasu da ake zargin masu kwacen waya sun caka mata wuƙa a cikin gidanta da dare
- Wani dan uwanta ya ce lamarin ya faru ne a daren Juma’a, yayin da aka shirya gudanar da jana’izarta a Masallacin Juma’a na Bolari da ke Gombe
- Har yanzu babu wani rahoto daga jami’an tsaro da ya tabbatar da kama wadanda ake zargi da hannu a kisan ko bayyana cikakken abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe – Wata mata da aka bayyana da suna Ai Ibrahim ta rasu bayan wasu da ake zargin masu kwacen waya sun caka mata wuƙa a cikin gidanta da dare.
Hakan na zuwa ne duk da cewa gwamnatin jihar ta dakatar da zirga-zirga da babur a jihar da dare domin kaucewa matsalar barayi da sauransu.

Source: Facebook
Dan uwar marigayiyar, Ayuba Muhammad Lawan da ya bayyana labarin a Facebook ya sanar da lokacin da za a mata jana'iza.
An caka mata wuƙa a gidanta
Abokin kanin marigayiyar Usman Saleh, ya wallafa Facebook cewa Ai ta rasu ne sakamakon harin da wasu da ake zargin masu kwacen waya suka kai mata.
Ya bayyana cewa an caka mata wuƙa har ta mutu, lamarin da ya jefa ’yan uwa da abokan arziki cikin jimami.
Wasu bayanai da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa an tabbatar da rasuwar tare da cewa lamarin ya faru ne a cikin gidanta a daren Juma’a.
Za a yi jana’izarta a Bolari
An bayyana cewa za a gudanar da jana’izar mamaciyar a yau Asabar da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Za a gudanar da sallar jana’izar a Masallacin Juma’a na Bolari, inda aka bukaci jama’a da su halarta domin yi mata addu’a.

Kara karanta wannan
"Zan iya rantsewa," Tsohon gwamna ya ce bai taba ganin shugaba kai tsari kamar Tinubu ba
’Yan uwa da abokan arziki sun yi ta wallafa sakonnin ta’aziyya da addu’ar Allah Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya jikanta da rahama.
Iyayen marigayiyar suna zaune ne a unguwar Pantami Yamma, kusa da Kwanalar Filato, duk da cewa ba a samu rahoto kan wajen da aka kashe ta ba.
Ta bar ’ya’ya biyar kanana
Usman Saleh ya bayyana cewa mamaciyar ta bar ’ya’ya biyar kanana, yana addu’ar Allah Ya ba su da sauran iyalanta hakurin jure babban rashi.
Ya kuma bayyana alhininsa kan yadda ya ce sun hadu da ita shekaru kadan da suka wuce, inda ta yi masa wasa da zolaya cikin farin ciki.

Source: Original
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu wani bayani daga jami’an tsaro da ke tabbatar da yadda lamarin ya faru ko matakin da aka dauka kan wadanda ake zargi ba.
An yi nade-nade a Gombe
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya amince da nada kwamishinoni uku, masu ba shi shawara na musamman biyu da manyan mataimaka na musamman hudu.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Njodi, ya bayyana cewa an tura sunayen kwamishinonin da aka zaba zuwa Majalisar Dokokin Jihar Gombe domin tantancewa da amincewa.
Sunayen kwamishinonin da aka gabatar sun hada da Dakta Ahmed Doho, Nasiru Degri da Dakta Muhammad A. Bello.
Asali: Legit.ng

