Atiku Ya Ragargaji Tinubu kan Tafiya Hutu Turai 'Najeriya na Ci da Wuta'

Atiku Ya Ragargaji Tinubu kan Tafiya Hutu Turai 'Najeriya na Ci da Wuta'

  • Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan tafiyarsa Turai domin hutun mako uku
  • Atiku ya ce Najeriya ba ta karkashin cikakken kundin tsarin mulki, sai dai tana fuskantar wani babban gibi na shugabanci a yanzu
  • Ya bayyana cewa tafiyar Tinubu ta zo ne a lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, tsadar man fetur, tashin kuɗin sufuri da matsalar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana rashin amincewarsa da matakin Shugaba Bola Tinubu na tafiya Turai domin hutu na mako uku.

A cewarsa, akwai bambanci tsakanin tafiyar ɗan ƙasa mai zaman kansa da kuma nauyin da ke kan shugaban da ke jagorantar ƙasar.

Kara karanta wannan

'Akwai gagarumar matsala': Malamin addini ya bukaci Tinubu ya hakura da takara

Atiku Abubakar da Bola Tinubu
Bola Tinubu a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Paul Ibe|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Atiku ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, inda ya ce matsalar ba wai Tinubu ba shi da ‘yancin yin hutu ko tafiya ƙasashen waje ba ce, sai dai lokacin da ya zaɓa domin yin hakan.

‘Gidansa na ci da wuta’

Atiku ya kwatanta halin da Najeriya ke ciki da wani uba wanda zai iya tafiya daga gida idan komai yana tafiya yadda ya kamata, amma ba zai ɗauki akwatinsa ya nufi filin jirgin sama ba idan gidansa na ci da wuta kuma iyalansa suna ciki.

Ya ce matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta sun haɗa da tsadar man fetur, tsadar rayuwa, tashin kuɗin sufuri da kuma rashin tsaro da ke haddasa mutuwar mutane a kai a kai.

Ya ce a irin wannan yanayi, shugaban ƙasa ya kamata ya kasance a gida domin tunkarar matsalolin ƙasar.

Kara karanta wannan

Atiku zai bambanta da Tinubu, ya yi albishir ga matasa da ya gana da yan N Power

Atiku ya rubuta cewa:

“Ku duba abin da Bola Tinubu ya bari a baya. Man fetur ya wuce ƙarfin talakawa. 'Yan Najeriya sun rage samun abinci. Kuɗin sufuri ya sa tafiya zuwa ƙauye kamar kayan gabas. Rashin tsaro na ya turnuke ‘yan Najeriya. Ana tsaka da haka, Shugaba Tinubu ya tattara kayansa ya tafi Turai hutun mako uku.”
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na magana a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Karin sukar Atiku ga Tinubu

Atiku ya ƙara da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ma yana ƙasar waje, abin da ya ce ya ƙara sanya wa ba za a fahimci manufar tafiyar Tinubu ba.

Tribune ta wallafa cewa Atiku ya ce:

“Uba na iya tafiya idan komai yana cikin kwanciyar hankali. Amma idan rufin gidansa na ci da wuta kuma iyalansa suna ciki, ba zai ɗauki akwatinsa ya nufi filin jirgin sama ba."

'Tinubu ya firgita,' ADC

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar ADC ta bayyana shirin gwamnatin tarayya na dala biliyan ɗaya na tallafa wa jama’a a a matsayin ta shiga rudani.

Kara karanta wannan

'Malaman tsibbunka ne suka jawo maka': Fadar shugaban kasa ta dura kan Atiku

Jam’iyyar ta zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin talauci ta hanyar manufofin tattalin arziƙin da ta kira marasa nasara.

ADC ta kuma tambayi inda gwamnati ta samo kuɗin shirin bayan shekaru uku tana gaya wa ‘yan Najeriya su jure wahalhalun tattalin arziƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng