Makusantan El Rufai Sun Fara Magana kan Zargin Sun Yi Watsi da Tsohon Gwamnan
- Muktar Isa-Hazo ya ce har yanzu yana daga cikin abokan Nasir El-Rufai, amma sun bambanta wajen ra’ayin siyasa da kuma tsarin da za su bi a zaɓen 2027
- Isa-Hazo ya ce wasu mutanen da yanzu suke bayyana kansu a matsayin makusantan El-Rufai, a baya ba su goyon bayansa, yana zargin suna amfani da sunansa
- Tsohon ɗan majalisar ya kuma zargi wasu ’yan gidan El-Rufai da ba shi bayanan da ba su dace ba yayin da yake tsare, amma bai gabatar da hujjar wannan zargi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Tsohon mataimakin kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Alhaji Muktar Isa-Hazo, ya ce abokan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ba su yi watsi da shi ba.
Mukhtar Isa-Hazo, wanda ya wakilci mazabar Basawa a majalisar, ya ce wasu daga cikin mutanen da suka kasance kusa da El-Rufai sun bar shi ne a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), tare da wasu da a baya ba sa goyon bayansa.

Kara karanta wannan
El Rufai ya aika sako ga 'yan uwa da abokan arziki bayan shafe fiye da kwanaki 200 a tsare

Source: Twitter
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da jaridar Leadership ranar Juma’a, 25 ga watan Satumban 2026.
Sun raba gidan siyasa da El-Rufai
Ya ce har yanzu shi abokin El-Rufai ne, amma sun bambanta a siyasance yayin da ake tunkarar zaɓen 2027. Isa-Hazo ya ce babu wanda ya yi watsi da El-Rufai
Isa-Hazo ya mayar da martani kan kalaman El-Rufai cewa wasu daga cikin abokansa da mutanen da suke tare da shi sun yi nesa ko sun yi shiru yayin da yake fuskantar shari’a.
Tsohon ɗan majalisar ya ce babu wanda ya yi watsi da tsohon gwamnan, yana mai cewa mutanen da El-Rufai ya fi buƙata sun kasance tare da shi a lokacin da ake buƙatarsu.
“Har yanzu ni abokin El-Rufai ne, amma kawai mun bambanta wajen tsarin siyasa. Babu wanda ya yi watsi da tsohon gwamna Nasir El-Rufai; lokacin da abin ya fi muhimmanci, mutanen da yake buƙata sun kasance tare da shi,” in ji shi.
Sai dai Isa-Hazo ya ce wasu mutanen da yanzu suke ikirarin suna tare da El-Rufai na iya kasancewa suna amfani da matsayinsa ne domin cimma wasu manufofinsu na siyasa.
Ya ce wasu sun koma APC
Isa-Hazo ya bayyana cewa wasu daga cikin mutanen da suke tare da El-Rufai sun koma jam’iyyar APC ne saboda wasu da a baya suka yi adawa da tsohon gwamnan yanzu suna ƙoƙarin kusantar sa.
Ya ce waɗanda suka koma APC suna ganin wannan tsarin ya fi dacewa, yayin da wasu mutanen da suka kasance kusa da El-Rufai na gaske suke ganin hakan bai dace ba.
Tsohon mataimakin kakakin majalisar ya kuma yi zargin cewa El-Rufai na iya samun bayanai daga mutanen da suke kusa da shi a yanzu, saboda kasancewarsa a tsare.
Isa-Hazo ya zargi wasu da yi wa El-Rufai bayanai Isa-Hazo ya yi zargin cewa wasu daga cikin ’yan gidan El-Rufai da ke ganinsa a lokacin da yake tsare na iya kasancewa suna isar masa da bayanai kan abubuwan da ke faruwa.
Ya ce saboda haka, abin da El-Rufai ke ji daga waɗannan mutanen na iya shafar yadda yake kallon sauye-sauyen siyasa da dangantakarsa da tsofaffin abokansa.
Sai dai wannan zargi na Isa-Hazo ne, kuma bai gabatar da wata hujja da ta tabbatar da cewa ’yan gidan El-Rufai suna ba shi bayanan da ba su dace ba ba.
Ya ce El-Rufai bai tuntubi wasu abokansa ba
Isa-Hazo ya kuma ce El-Rufai bai taɓa kiran wasu daga cikin mutanen da suke tare da shi domin ba su umarni ko bayyana musu sabon tsarin siyasar da yake so su bi ba.
“Gaskiya ina gaya muku yanzu, mu da muke tare da shi, bai taɓa kiranmu ya ce ga inda nake son mu dosa ba. A wannan lokacin, kowane mutum yana bin abin da yake ganin ya dace da shi. Shi ke nan,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa sauyin tsarin siyasa ne ya sa wasu daga cikin abokan El-Rufai suka ɗauki hanyoyi daban-daban, ba wai sun yi watsi da shi ba.
Wasu abokan El-Rufai ba su mayar da martani ba
An tuntubi wasu daga cikin abokan El-Rufai da suka haɗa da tsohon Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarauta, Sani Jafaru, da tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati kuma Kwamishinan Kuɗi, Sa’idu Bashir.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Sai dai, ba su amsa kiran waya ko mayar da saƙonnin da aka aika musu ba domin jin matsayinsu kan zarge-zargen cewa sun yi watsi da tsohon gwamnan.

Source: Facebook
Jigo a APC ya roki Tinubu kan El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar APC, Denge Josef Onoh, ya aika sako ga Shugaba Bola Tinubu kan Nasir El-Rufai.
Jigon na APC ya roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sa baki kan shari’o’in da tsohon gwamnan na jihar Kaduna ke fuskanta.
Asali: Legit.ng

