Bayanai Sun Fito kan Yadda FBI Ta Taba Bincikar Atiku, Lalube Gidansa a 2005

Bayanai Sun Fito kan Yadda FBI Ta Taba Bincikar Atiku, Lalube Gidansa a 2005

  • FBI ta binciki gidan Atiku Abubakar a Maryland a ranar 3 ga Agusta, 2005, lokacin yana mataimakin shugaban Najeriya, a wani bincike kan ɗan majalisar Amurka
  • Binciken ya shafi William Jefferson, ɗan majalisar Amurka daga New Orleans, da zargin biyan ko shirya biyan kudi ga jami’an Najeriya da Ghana
  • Jefferson na ƙoƙarin tallata wata yarjejeniyar sadarwa a Najeriya, yayin da lauyansa ya ce FBI na gudanar da wani samame na musamman a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Washington, D.C. - An sake bayyana wasu bayanai kan yadda jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) suka kai samame gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, a Maryland.

Lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Agusta, 2005, lokacin da Atiku ke rike da mukamin mataimakin shugaban Najeriya a gwamnatin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo.

Kara karanta wannan

Trump ya ba mutumin Atiku mukami a gwamnatin Amurka ana shirin zaben 2027

FBI ta taba yin bincike kan Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar da tambarin hukumar FBI Hoto: Pius Utomi EKPEI / AFP
Source: Getty Images

Rahotannin NBC, New York Times da wasu manyan kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa binciken yana da alaka da wani bincike da hukumomin Amurka ke yi kan ɗan majalisar wakilan Amurka, William Jefferson.

Binciken ɗan majalisar Amurka

A cewar rahoton New York Times, binciken ya mayar da hankali kan Jefferson, wani ɗan jam’iyyar Democrat daga New Orleans.

Jami’an gwamnatin Amurka sun binciki wasu takardu da suke zargin za su iya nuna ko Jefferson ya biya, ya yi tayin biya ko kuma ya ba da izinin biyan kudi ga wasu jami’an Najeriya ko Ghana.

Takardun binciken sun nuna cewa jami’an sun fi mayar da hankali kan alakar Jefferson da Atiku Abubakar, da kuma Aliu Mahama, wanda a lokacin yake mataimakin shugaban Ghana.

Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani

A lokacin da lamarin ya faru, Atiku bai samu damar yin magana da manema labarai kan samamen ba.

Kara karanta wannan

Wasikar da Amurka ta aiko Najeriya ta bayyana ainihin shekarun Tinubu a duniya

Sai dai wata mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa gwamnati ta samu labarin abin da ya faru kuma tana kokarin gano dalilin samamen.

Ta ce, kamar yadda tashar NBC ta ruwaito:

“An sanar da fadar shugaban kasa lamarin, kuma tana amfani da hanyoyin diflomasiyya domin gano dalili da sakamakon abin da ya faru.”

Amurka ta tabbatar da binciken gidan Atiku

Wani jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar da cewa an binciki gidan Atiku da ke Potomac, wani yanki da ke kusa da Washington.

Sai dai jami’in ya mayar da sauran tambayoyi ga Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, wadda ta ki yin karin bayani kan lamarin.

Wani bangare na takardun da aka nema ya shafi wata yarjejeniyar harkar sadarwa da Jefferson ke kokarin ganin an aiwatar da ita a Najeriya.

Kamfanin iGate na neman shigowa Najeriya

Majiyoyi sun bayyana cewa Jefferson yana kokarin samar da damar da kamfanin iGate Corp., wani kamfanin da ke Kentucky, zai shigar da fasahar intanet mai saurin gaske cikin kasuwar sadarwa ta Najeriya.

A wancan lokaci, bangaren sadarwa na Najeriya yana cikin saurin bunkasa, lamarin da ya sa kasuwar ta zama abin sha'awa ga kamfanonin fasahar sadarwa na kasashen waje.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin ’yan ta’adda 2 a Katsina

Jefferson ya kuma dawo daga Ghana ne bayan tafiyar kwanaki biyar a tsakiyar watan Yulin 2005, 'yan makonni kafin FBI ta kai samamen gidan Atiku.

Matsayar William Jefferson

Melanie Roussell, mai magana da yawun Jefferson, ta ce ɗan majalisar ba zai yi tsokaci kan binciken ba.

Sai dai ta tabbatar da cewa Jefferson yana ba jami’an bincike hadin kai. Lauyansa, Mike Fawer, ya kuma yi nuni da cewa FBI na iya gudanar da wani samame na musamman domin tattara hujjoji kan Jefferson.

An taba bincikar gidan Atiku a Amurka
Atiku Abubakar a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: @atiku
Source: Twitter

An ba mutumin Atiku mukami a Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump ya nada Karl-Marx Edward Ikemefuna William George Okeke-Von Batten mukami.

Majiyoyi suka ce mutumin wanda aka fi sani da Karl Von Batten an nada shi a matsayin kwamishina a wata hukuma a fadar White House.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng