Mutuwa Ta Girgiza Dan Takarar Gwamna, Mutum 6 daga Cikin Mutanensa Sun Rasu Lokaci 1

Mutuwa Ta Girgiza Dan Takarar Gwamna, Mutum 6 daga Cikin Mutanensa Sun Rasu Lokaci 1

  • Yan siyasa magoya bayan ɗan takarar gwamnan SDP a Nasarawa, Mohammed Abubakar Adamu, sun yi hatsari yayin tafiya zuwa wani taron siyasa
  • Mutane shida sun rasa rayukansu a hatsarin da ya afku a kan gadar sama da ke Lafia, yayin da wasu da dama suka jikkata
  • Gwamnatin Nasarawa da APC sun jajanta wa iyalan mamatan tare da kira ga masu ababen hawa da su kiyaye dokokin hanya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa, Nigeria - Magoya bayan ɗan takarar gwamnan jam’iyyar SDP a jihar Nasarawa kuma tsohon Sufeto-Janar na ’yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, shida sun mutu a wani hatsarin mota.

Hatsarin ya afku ne ranar Litinin a kan gadar sama da ke Lafia, yayin da yan siyasar ke kan hanyarsu ta zuwa wani taron siyasa a ƙaramar hukumar Awe.

Kara karanta wannan

Abin ba daɗi: Yan bindiga sun mamayi wasu bayin Allah, sun buɗe wa motarsu wuta

Adamu.
Tsohon sufeto janarna rundunar yan sandan Najeriya, Muhammed Adamu a wurin rabon tallafi a Nasarawa Hoto: Wambo Samuel
Source: Facebook

Daraktan yaɗa labarai da dabarun sadarwa na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen tsohon IGP, Otaru Douglas, ya tabbatar wa Daily Trust faruwar hatsarin, inda ya ce wasu magoya baya da dama sun samu raunuka.

Ya ce:

“Addu’armu ita ce Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma ba waɗanda suka samu raunuka sakamakon hatsarin lafiya cikin gaggawa.”

Matar tsohon IGP ta yi alhini

Matar Adamu, Hajiya Rukayya, ta jagoranci wata tawaga zuwa gidajen mamatan, inda ta jajanta wa iyalansu tare da yi musu addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan.

Gwamnatin jihar Nasarawa ma ta jajanta wa ɗan takarar SDP da iyalan waɗanda hatsarin ya rutsa da su.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Al’adu da Yawon Buɗe Ido, Dakta Nawani Aboki, ya bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, inda ya buƙaci masu yaƙin neman zaɓe da masu ababen hawa su yi taka-tsantsan a kan tituna.

“Abin baƙin ciki ne cewa mun rasa mutane a hatsarin. Gwamnati na ci gaba da jimamin rasuwarsu tare da iyalansu. Wannan ba batun jam’iyya ba ne; batun mutane ne, ’yan ƙasar Nasarawa,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Tinubu, Atiku da Peter Obi sun bayyana hanyar da suka samu dukiyoyinsu

Aboki ya buƙaci jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su tabbatar da an kiyaye lafiyar jama’a yayin tafiye-tafiyen yaƙin neman zaɓe.

SDP .
Tambarin jam'iyyar adawa ta SDP a Najeriya Hoto: SDP Danja
Source: Facebook

Jam'iyyar APC ta yi ta'aziyya

Jam'iyyar APC mai mulki ta jihar Nasarawa ta bi sahun masu aika sakon ta'aziyya, inda ta bayyana alhininta kan hatsarin, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaranta, Augustine Ogaba, ya fitar, jam’iyyar ta bayyana hatsarin a matsayin wani lamari mara raɗaɗi, tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da kuma magoya bayan SDP.

Yadda Adamu ya samu tikitin SDP

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu, ya zama ɗan takarar gwamnan Nasarawa a zaben 2027 karkashin inuwar SDP.

Kwamitin zaɓen SDP ya ce wakilai 28,637 sun kada kuri’a, inda Adamu ya samu mafi yawan ingantattun kuri’u a zaɓen da aka gudanar cikin lumana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262