Wasikar da Amurka Ta Aiko Najeriya Ta Bayyana Ainihin Shekarun Tinubu a Duniya
- Wata wasika ta shekarar 2003 daga Ofishin Jakadancin Amurka ta bayyana sakamakon binciken bayanan laifuka da aka yi wa Bola Tinubu
- Binciken FBI ta hanyar National Crime Information Centre bai gano wani bayanin kama Tinubu, sammacin kama shi ko neman sa ruwa a jallo ba
- Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Reno Omokri, ya wallafa takardar, inda ya jawo hankali kan ranar haihuwar da aka rubuta wa Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Wata wasika daga Ofishin Jakadancin Amurka mai kwanan wata 4 ga Fabrairu, 2003, ta sake bayyana a kafafen sada zumunta, inda aka rubuta ranar haihuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wasikar ta ƙunshi sakamakon binciken bayanan laifuffuka da hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka, FBI ta gudanar kan Tinubu ta hanyar cibiyar NCIC.

Source: Twitter
Reno Omokri ya wallafa takardar
Reno Omokri, wanda aka bayyana a matsayin jakada mai jiran naɗi kuma tsohon hadimin shugaban ƙasa, ne ya wallafa takardar a shafinsa na X.
Michael H. Bonner, jami’in kula da harkokin shari’a a Ofishin Jakadancin Amurka da ke Legas, ne ya rubuta wasikar zuwa ga Tafa Balogun, wanda a lokacin yake matsayin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya.
An rubuta wasikar ne a matsayin martani ga wata buƙata da Balogun ya aika ranar 3 ga Fabrairu, 2003, yana neman bayanai kan Tinubu daga cibiyar NCIC ta FBI.
Takardar tana ɗauke da hatimin kwafin sahihiyar takarda daga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuffukka Masu Alaƙa (ICPC) da ke Jihar Legas.
Wasikar ta fadi ranar haihuwar Tinubu
A cikin wasikar, Bonner ya shaida wa Balogun cewa binciken da aka gudanar ta NCIC bai gano wani bayanin kama Bola Ahmed Tinubu bisa laifi, wani sammacin kama shi da ake nema ko sanarwar neman sa ruwa a jallo ba.
Wasikar ta kuma nuna cewa an gudanar da bincike kan Tinubu, wanda ta ce an haife shi a ranar 29 ga watan Maris, 1952.

Kara karanta wannan
EFCC ta kama mutum 2 'yan Najeriya, ta mika su ga Amurka saboda laifin da suka aikata
Bonner ya bayyana NCIC a matsayin wata babbar cibiyar bayanai da ke tattara bayanan kama mutane da hukuncin da aka yanke musu daga sassa daban-daban na Amurka da yankunanta.
A cewar takardar:
“Sakamakon binciken bai gano wani bayanin kama Bola Ahmed Tinubu kan aikata laifi, wani sammacin kama shi ko sanarwar neman sa ruwa a jallo ba, wanda aka rubuta ranar haihuwarsa a matsayin 29 ga Maris, 1952.”

Source: Twitter
Abin da NCIC ke kunshe da shi
NCIC wata cibiyar bayanan laifuffukka ce ta ƙasa da hukumar FBI ke gudanarwa a Amurka.
Saboda haka, rashin gano wani bayani a NCIC yana nufin kawai cewa babu bayanin laifuka da aka samu a Amurka a lokacin da aka gudanar da binciken.
Ranar haihuwar Tinubu ta daɗe tana zama batun muhawara a Najeriya, lamarin da ya sa ranar 29 ga Maris, 1952, da aka rubuta a cikin wannan takarda ta Ofishin Jakadancin Amurka ta ja hankalin masu bibiyar wannan batu.
Amurka ta taba bincikar Tinubu
Kun ji cewa hukumar FBI ta Amurka tabbatar cewa an taɓa gudanar da bincike kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Ta ce kotun Amurka ta riga ta tabbatar da cewa an taɓa samun amincewar hukuma kan binciken da aka gudanar a kan Shugaba Tinubu.
Asali: Legit.ng
