Asiri Ya Kara Tonuwa: Majalisa Ta Gano Hukumomin Bogi 12 da Kafa a Mulkin Tinubu
- Kwamitin bincike na wucin gadi da Majalisar Wakilai ya mika rahotonsa kan hukumar bogi da ake ta surutu a janta, PFIPC
- Kwamitin Majalisar ya tabbatar da cewa hukumar ta bogi ce, kuma takardar nadin Adeyemi Adeniyi a matsayin shugaba ta bogi ce
- Masu binciken sun gano wasu hukumomi 12 da ake zargin suna aiki ba bisa ka'ida ba tare da asusun banki 58 da ake alakanta su da Adeyemi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken ayyukan hukumar da ake kira Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC) ya fitar da rahotonsa.
Kwamitin ya bayyana PFIPC a matsayin wata hukumar gwamnati ta bogi, wacce aka kafa ba tare da amincewar doka ba.

Source: Facebook
Ledership ta rahoto cewa kwamitin Majalisar ya kuma yanke cewa takardar da ake ikirarin an nada Adeyemi Adeniyi a matsayin Darakta Janar na PFIPC takarda ce ta bogi.
Wannan na cikin sakamakon binciken farko da kwamitin ya fitar ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, 2026
Majalisa ta wanke Gbajabiamila
Shugaban kwamitin, Hon. Ibrahim Sani Madaki, ya ce binciken da aka gudanar zuwa yanzu ya wanke Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, daga zargin hannu a ayyukan PFIPC.
Madaki ya yaba wa Gbajabiamila saboda sanar da hukumomi game da samuwar hukumar da ayyukanta.
Ya ce matakin Gbajabiamila ya taimaka wajen gano abin da kwamitin ya bayyana a matsayin wata hanyar kafa kungiyoyin bogi da ke bayyana kansu a matsayin hukumomin gwamnati.
An gano wasu hukumomin bogi 12
A cewar kwamitin, masu bincike sun gano wasu kungiyoyi 12 da ake zargin suna gudanar da ayyuka ba bisa ka'ida ba tare da amfani da sunayen hukumomin gwamnati duka a karkashin Adeyemi.
'Yan majalisar sun kuma bayyana cewa an alakanta asusun banki 58 da Adeniyi dangane da kungiyoyin da ake bincike.
Daga cikin hukumomin bigi da aka gano akwai FCT Investment Promotion Council, FCT Investment Promotion Agency and Public-Private Partnership, United Nations Youth Global Foundation da Olubadan of Ibadan Foundation.

Source: Facebook
Kwamitin ya ce gano wadannan hukumomi ya haifar da damuwa mai tsanani kan ayyukan mutane da kungiyoyin da ake zargin suna gabatar da kansu a matsayin sahihan hukumomin gwamnati yayin da suke gudanar da ayyuka ba tare da izini ba.
Kwamitin ya kara da cewa zai gabatar da wasu shawarwari bayan kammala bincikensa kan PFIPC da sauran kungiyoyin da aka gano, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Dalilin ICPC na wanke Femi Gbajabiamila
A wani labarin, kun ji cewa ICPC ta kammala binciken ta game da zargin Femi Gbajabiamila da nadin Adeniyi Adeyemi a matsayin shugaban wata hukumar bogi
Binciken ya nuna cewa Adeyemi ne ya ƙirƙiri takardar nadin kansa tare da amfani da takardar kai ta fadar shugaban ƙasa da sa hannun Gbajabiamila.
Binciken ICPC ya ce an yi amfani da takardar aiki ta bogi mai kama da ta Fadar Shugaban Ƙasa wajen ƙirƙirar takardar, sannan aka jingina sa hannun Gbajabiamila a kanta.
Asali: Legit.ng

