Atiku Ya Dauki Alkawarin da Zai Faranta wa Daliban Najeriya Rai kan Kudin NELFUND
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai sake duba tsarin NELFUND tare da yafe basussukan ilimi ga ɗaliban da suka cancanta
- Atiku ya ce bai kamata matasan Najeriya su fara rayuwar aiki da nauyin bashin karatu wuyansu ba
- Mai magana da yawunsa ya zargi Tinubu da ƙara tsadar ilimi sannan ya gabatar da rancen karatu a matsayin mafita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sake gyara tsarin Asusun Bayar da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) tare da yafe basussukan karatu ga ɗaliban Najeriya da suka cancanta.
Atiku ya kuma yi watsi da abin da ya kira ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na amfani da shirin NELFUND a matsayin hujjar cewa ilimi ya zama mai sauƙin biya a ƙarƙashin gwamnatinsa.

Source: Facebook
Babban mataimaki na musamman ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar kan hulɗa da jama'a, Phrank Shaibu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitara shafin X da yammacin Talata.
Shaibu ya ce martanin nasa ya biyo bayan wani saƙo da Shugaba Tinubu ya fitar, inda shugaban ya soki manufofin tattalin arzikin Atiku ba tare da ambaton sunansa kai tsaye ba.
Atiku ya soki tsarin NELFUND
Shaibu ya ce amfani da NELFUND da Tinubu ya yi wajen kare kansa daga shawarar Atiku ta rage tsadar makamashi ba gaskiya ba ne.
Ya ce shugaban ƙasar ya fara ƙara tsadar ilimi kafin daga bisani ya gabatar da lamunin karatu a matsayin hanyar ceto ɗalibai.
Ya ce:
“Amfani da NELFUND a matsayin hujjar cewa ilimi ya zama mai sauƙi ƙarƙashin gwamnatinku tamkar ka ƙona kuɗin makaranta ne sannan ka yi taƙama cewa ka ba ɗalibai bokitin ruwa don kashe wutar.
"Menene hikimar gwamnati yayin da ake samun ƙarin tsadar kuɗin makaranta sosai a wasu cibiyoyi, sannan daga baya a yi murnar lamuni a matsayin mafita?”
Ya kara cewa gwamnati ta ƙara wa ilimi tsada da hannu ɗaya, sannan ta bai wa ɗalibai bashi da ɗayan hannun domin su iya jure ƙarin tsadar, daga bisani kuma ta nemi a yaba mata kan taimakon.
Alkawarin Atiku ga daliban Najeriya
A cewar Shaibu, Atiku ya riga ya sake duba tsarin lamunin ɗalibai da ake amfani da shi, kuma bai yarda matasan Najeriya su fara rayuwar aiki da nauyin bashin ilimi ba.
Ya ce Atiku zai rage tsadar ilimi, sannan bayan sake duba tsarin, ya yafe basussukan ɗaliban da suka cancanta domin matasan Najeriya su kammala karatunsu cikin fata maimakon ɗaukar nauyin biyan bashi.

Source: Facebook
Shaibu ya kuma zargi fadar shugaban ƙasa da amfani da dabarun tsoratar da ɗalibai da ma’aikatan Najeriya, ta hanyar nuna cewa shirin Atiku na rage tsadar mai zai iya shafar NELFUND da albashin ma’aikata.
Abin da ya hana Atiku zuwa taron G100
Kun ji cewa jam’iyyar ADC ta yi bayani kan dalilin da ya sa ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, bai halarci taron G-100 na jam’iyyun adawa ba.
Jam’iyyar ta ce taron ya fi mayar da hankali ne kan tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasa da neman hanyoyin haɗin gwiwa, ba tattaunawar ’yan takarar shugaban ƙasa ba.
Asali: Legit.ng

