Shin da Gaske Atiku Zai Sayar da Bankin CBN idan Ya Zama Shugaban Kasa?
- Wani hoton labari da ke yaɗuwa ya yi ikirarin cewa Atiku Abubakar zai sayar da Babban Bankin Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa.
- An gudanar da bincike domin gano gaskiya kan ikirarin da aka yada dangane da dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar ADC
- Mataimakin Atiku ya ce ikirarin ƙarya ne, yana mai cewa CBN hukuma ce ta kuɗi da doka ta kafa, ba kadarar kasuwanci da za a sayar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani hoto da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce zai sayar da Babban Bankin Najeriya (CBN) idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na African Democratic Congress (ADC), ya kasance ana yaɗa wasu maganganu da ake danganta masa a yayin da ake ƙara kusantar zaɓen 2027.

Source: Facebook
Sai dai binciken da aka gudanar ya nuna cewa babu wata hujja da ke tabbatar da cewa Atiku ya taɓa yin wannan magana.
Yadda ikirarin ya yaɗu
Wani mai amfani da X mai suna @Sistaliano ne ya wallafa hoton a ranar Lahadi, inda aka rubuta cewa:
“Zan sayar da Babban Bankin Najeriya idan aka zaɓe ni. Wasu ƙasashe sun taɓa yin hakan a baya – Atiku Abubakar.”
An danganta maganar da jaridar Sahara Reporters, kuma hoton ya samu dubban wadanda suka gan shi a X.
Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta ma sun sake yaɗa ikirarin, lamarin da ya sa ya samu karɓuwa a tsakanin jama’a.
Babu rahoton da ya tabbatar da maganar
Binciken Cable Check ya nuna cewa ba a samu wani rahoto a shafin Sahara Reporters da ke tabbatar da cewa Atiku ya yi wannan magana ba.
An kuma gano cewa hoton da ke yaɗuwa ya bambanta da tsarin hotunan da Sahara Reporters ke amfani da su wajen wallafa labaransu.
Haka kuma, babu wani faifan bidiyo, sanarwa ko saƙon Atiku ko jam’iyyar ADC da ya tabbatar da wannan ikirari.
Ba a kuma samu rahotanni daga manyan kafafen yaɗa labarai da suka danganta wannan magana ga Atiku ba.
Mataimakin Atiku ya musanta ikirarin
Phrank Shaibu, babban mataimaki na musamman ga Atiku kan harkokin sadarwa, ya bayyana ikirarin a matsayin ƙarya.
Shaibu ya ce Atiku bai taɓa cewa zai sayar da CBN idan ya zama shugaban ƙasa ba.
Ya bayyana CBN a matsayin hukuma ta kuɗi da doka ta kafa, ba wata kadarar kasuwanci ta gwamnati da za a iya sayarwa ba.
A cewarsa, Atiku ya kasance yana magana ne kan ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, dawo da ‘yancin CBN da kuma amincewar jama’a ga harkokin kuɗi. Ya ce bai kamata a rikita waɗannan manufofi da batun sayar da CBN ba.
Shin ana iya sayar da babban banki?
Manyan bankunan ƙasashe galibi hukumomin gwamnati ne da ke gudanar da muhimman ayyukan ƙasa, ciki har da fitar da kuɗi, kula da ajiyar kuɗaɗen waje da tsara manufofin kuɗi.

Kara karanta wannan
Shirin dawo da tallafin man fetur ya firgita shugaban APC, ya fadi illar shirin Atiku
Wasu ƙasashe kaɗan suna da tsarin da wasu masu zaman kansu ke riƙe da hannun jari a babban bankinsu, amma hakan ba ya ba su ikon tafiyar da manufofin kuɗi ko gudanar da bankin.
Saboda haka, batun sayar da babban banki ga masu zaman kansu na iya fuskantar manyan matsalolin doka, kundin tsarin mulki da kuma manufofin kuɗi.
Me binciken ya gano?
Babu wata hujja da ke nuna cewa Atiku Abubakar ya ce zai sayar da Babban Bankin Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa a 2027.
Binciken ya kuma nuna cewa babu wani rahoton Sahara Reporters da ya tabbatar da maganar, yayin da mataimakin Atiku ya fito fili ya musanta ikirarin.

Source: Facebook
Atiku ya yi wa 'yan Najeriya alkawari
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi alkawari kan kananan hukumomi.
Atiku ya yi alkawarin tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomin Najeriya suna isa gare su kai tsaye idan ya lashe zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng

