Wike Ya Fara Karaya, Ya Fadi Abin Atiku ko Obi Za Su Yi Masa idan Suka Ci Mulki

Wike Ya Fara Karaya, Ya Fadi Abin Atiku ko Obi Za Su Yi Masa idan Suka Ci Mulki

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce zai zama ɗan siyasar farko da Atiku Abubakar ko Peter Obi za su far wa bayan zaben 2027
  • Wike ya ce duk da kasancewarsa ɗan PDP, zai ci gaba da goyon bayan sake zaɓen Bola Tinubu kuma bai yi nadama ba
  • Ministan Abuja ya ce duk suka da kiraye-kirayen abokan hamayyarsa ba za su sa ya janye goyon bayansa ga Tinubu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana game da siyasar Najeriya musamman zaben shekarar 2027.

Wike ya ce zai zama ɗan siyasar farko da Atiku Abubakar, ko Peter Obi za su far wa idan Shugaba Bola Tinubu ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Wike ya dura kan Atiku da Obi
Peter Obi, Ministan Abuja, Nyesom Wike da Atiku Abubakar. Hoto: Mr Peter Obi, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Wike bai yi nadamar goyon bayan Tinubu ba

Kara karanta wannan

Minista ya kare Tinubu kan yadda gwamnoni ke kashe kudaden tallafin mai a Najeriya

Da yake magana a wani taron tattaunawa da manema labarai, ministan ya ce tsananin goyon bayan da yake bai wa Tinubu ya riga ya sanya shi cikin manyan mutanen da abokan hamayyarsa ke hari, cewar Punch.

Wike, wanda ya mayar da goyon bayan sake zaɓen Tinubu babban ɓangare na ayyukan siyasarsa, duk da kasancewarsa ɗan Jam’iyyar PDP, ya ce yana sane da sakamakon matsayar da ya ɗauka.

Ya ce:

“Ni ne ɗan siyasar farko da nake ganin za su fara nema. Ni ne ɗan siyasar farko. Na san za su zo neman kaina.”

Wike ya ce yiwuwar fuskantar sakamakon siyasa ba ta rage ƙudurin da yake da shi na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar ba, yana mai cewa bai yi nadamar bayyana goyon bayansa ga Tinubu ba.

Wike ya jaddada aniyarsa ta goyon bayan Tinubu
Ministan Abuja, Nyesom Wike yana jawabi a taro. Hoto: Lere Olayinka.
Source: Facebook

Kokarin da Wike ke yi wa Tinubu

Maimakon ya ja da baya daga fafatawar siyasa, ministan ya ce har yanzu ya mayar da hankali wajen tabbatar da cewa shugaban ƙasar ya samu wa’adi na biyu a kan karagar mulki.

Ya ce:

“Kowace rana idan na kwanta barci, ina tunanin sake zaɓen shugaban ƙasa. Idan ina cin abinci, ina tunanin sake zaɓen shugaban ƙasa. Duk abin da nake yi yanzu, game da sake zaɓen shugaban ƙasa ne.”

Kara karanta wannan

'Dole ku kawo yankunanku ga APC': Gwamna ya yi barazana ga ciyamomi

Tsohon gwamnan Rivers ya ce sukar da ake yi masa saboda matsayar siyasarsa ta kasance mai tsanani fiye da yadda aka saba.

Sai dai ya ce bai damu da sunayen da ake kiran sa da su ko ra’ayoyin da masu sukar sa ke bayyanawa ba.

Ya ce:

“Ban ga inda aka taɓa kiran wani mutum a wannan ƙasa da sunaye irin yadda ake kiran sunana ba. Ban damu da mutanen da suke faɗin nasu ra’ayin ba. Abin da ya shafe ni shi ne, kamar yadda na faɗa, zan goyi bayan Shugaban Ƙasa.”

Duk da cewa har yanzu ɗan PDP ne, yana goyon bayan Tinubu, ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki, a yaƙi da ’yan adawa ciki har da Atiku da Obi.

'Ba zan bari Atiku ya ci zabe ba' - Wike

Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce zai ci gaba da taka rawar gani a siyasar jihar Rivers gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Tsohon gwamnan ya ce ba zai zauna ya rike hannu bibbiyu ya bar Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa ba.

Wike ya ce yawan zuwa jiharsa ta Rivers da yake yi ba yana nufin zai bari Abuja ya dawo gida ua zauna ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.