Minista Ya Kare Tinubu kan Yadda Gwamnoni Ke Kashe Kudaden Tallafin Mai a Najeriya

Minista Ya Kare Tinubu kan Yadda Gwamnoni Ke Kashe Kudaden Tallafin Mai a Najeriya

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da ikon tambayat yadda jihohi da ƙananan hukumomi ke kashe kudadensu
  • Wike ya ce ya kamata Peter Obi ya tambayi yadda jihohi da ƙananan hukumomi ke amfani da kuɗaɗen da suke samu bayan cire tallafin mai
  • Tsohon gwamnan Rivers ya yaba wa Tinubu kan cire tallafin man fetur tare da buƙatar jihohi su yi bayani kan yadda suke kashe ƙarin kuɗaɗen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba shi da ikon gaya wa gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi yadda za su kashe ƙarin kuɗaɗen da suke samu bayan cire tallafin man fetur.

Wike ya bayyana haka ne ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, 2026 yayin wata ganawa da manema labarai a Fatakwal, jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND

Wike Tinubu.
Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da Shugana Bola Ahmed Tinubu Hoto: Nyesom Wike
Source: Twitter

Vanguard ta ce ya yi maganar ne yayin da yake mayar da martani kan kalaman tsohon gwamnan jihar Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, game da yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur.

Wike ya mayar da martani ga Obi

A cewar Wike, maimakon Peter Obi ya rika tambayar gwamnatin tarayya kawai, ya kamata ya kuma tambayi yadda gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ke amfani da ƙarin kuɗaɗen da suke samu.

Ya ce:

“Abin da kawai ya kamata ya tambaya shi ne, ‘Tun da an cire tallafin, me ake yi da kuɗaɗen da aka samu?’ Wannan shi ne abin da nake ganin mutum mai hankali ya kamata ya yi magana a kai.
“Yanzu gwamnati ta ce an raba kuɗaɗen da aka samu tsakanin gwamnatocin jihohi da sauran matakan gwamnati. Tinubu ba shi da ikon cewa, ‘Jiha, ga yadda za ku yi da kuɗaɗen da kuka samu daga cire tallafin man fetur.’

Kara karanta wannan

Shin da gaske Atiku zai sayar da bankin CBN idan ya zama shugaban kasa?

“Ba shi da ikon gaya wa ƙananan hukumomi yadda za su kashe kuɗinsu. Dukkan matakan gwamnati masu cin gashin kansu ne.”

Jihohi sun kamu karin kuɗi daga tarayya

Wike ya ce ƙarin kuɗaɗen da jihohi ke samu ya ba su damar gudanar da ayyuka fiye da yadda suke yi a baya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya ce wasu gwamnatocin jihohi da a baya suke fama da biyan albashi da fansho yanzu sun samu sauƙin gudanar da ayyukansu.

Wike.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @govwike
Source: Facebook

Ya ce:

“A yau jihohi suna cewa, sabanin baya da ba za mu iya biyan albashi ko fansho ba kuma ake fama da yajin aiki a ko’ina, yanzu babu irin waɗannan yajin aikin. Akwai fa’idoji. Yanzu ina da kuɗin gudanar da ayyuka.”

Wike ya dura kan Atiku, yan adawa

A baya, kun ji cewa Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya bayyana burinsa na kara wa Atiku Abubakar da yan adawa hawan jini a fagen siyasa kafin 2027.

Wike ya yi ikirarin cewa sauye-sauyen siyasa da ke faruwa za su haifar da babbar ƙawancen Rainbow Coalition na goyon bayan Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262