Kasashen Musulmi 2 Sun Kaure da Fada, an Yi Ruwan Bama Bamai
- Gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta ce za ta mayar da martani bayan hare-haren jiragen yakin Pakistan sun kashe akalla mutane hudu a kasar
- Pakistan ta ce ta kai hare-haren ne kan wurare 10 a Afghanistan da ake zargi ana ajiya da harba jiragen sama marasa matuka da ake kai hari da su
- Hare-haren sun kara dagula zaman lafiya tsakanin kasashen Pakistan da Afghanistan, yayin da kasashen biyu ke ci gaba da zargin juna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kandahar – Gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta yi barazanar mayar da martani bayan hare-haren jiragen yakin Pakistan sun kashe akalla mutum hudu a wasu sassan kasar.
Mai magana da yawun gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce hare-haren sun shafi lardunan Kandahar, Paktia da Khost.

Source: Getty Images
Pakistan ta ta kai hari Afghanistan
Al Jazeera ta wallafa cewa Pakistan ta ce a ranar Alhamis ta kai hare-hare ta sama kan wurare 10 a Afghanistan da ake amfani da su wajen adana da harba jiragen sama marasa matuka.
Ministan Yada Labarai na Pakistan, Attaullah Tarar, ya ce hare-haren sun kasance cikin shiri, an yi su daidai da wuraren da aka gano kuma an takaita su kan wuraren da ake alakanta su da hare-haren da aka yi yunkurin kai wa Pakistan.
Ya zargi wasu jiragen sama marasa matuka da kai hari cikin Pakistan ranar Laraba, yana mai cewa hakan ya kasance keta hurumin kasar da kuma wani mummunan hari da ba za a amince da shi ba.
Sai dai jami’an gwamnatin Taliban sun musanta cewa Afghanistan ce ta harba jiragen sama marasa matukan da aka kai wa Pakistan ranar Laraba.
An ji fashewa a Kandahar
Wani mazaunin birnin Kandahar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa jirgin yakin Pakistan ya kai hari a birnin da ke kudancin Afghanistan.
Mazaunin ya ce sun ji karar jirgin sama kafin wani babban fashewa, sannan wuta ta tashi a tsakiyar birnin Kandahar.
Mai magana da yawun Taliban ya ce hare-haren sun kashe akalla mutane hudu, tare da yin alkawarin cewa Afghanistan za ta mayar da martani da ya dace.
Barazana ga kokarin sulhu
Rikicin da ke kara kamari na iya kawo cikas ga kokarin China, Turkiyya, Qatar da Saudi Arabiya na shiga tsakani domin samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Pakistan da Afghanistan.
Dangantakar kasashen biyu ta kara tabarbarewa tun bayan kazamin fada da suka yi a watan Fabrairu, wanda ya kasance daya daga cikin mafi muni da aka gani tsakanin kasashen biyu cikin shekaru.

Source: Getty Images
Iran caccaki Trump
A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar Hafsan Hafsoshin Sojin Iran ta yi watsi da kalaman Shugaban Amurka Donald Trump na barazana ga Iran.
Rundunar ta ce Trump ya maimaita kalaman da take ganin suna nuna kiyayya da barazana ga Iran, tare da kokarin amfani da dandalin Majalisar Dinkin Duniya wajen bata Iran.
Ta ce irin wadannan kalamai ba su nuna karfin Amurka ba, a cewarta, illa dai abin da ta bayyana a matsayin matsanancin yanayi da Washington ke ciki sakamakon tsawaita rikici da Iran.
Asali: Legit.ng

