An Samu Abin da Ya Bambanta Tinubu, Atiku da Peter Obi gabanin Zaben 2027
- Ibrahim Abdulkarim ya ce Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar suna neman ikon siyasa, yayin da Peter Obi ke neman damar yi wa Najeriya hidima
- Jigon NDC ya ce matsalar Najeriya ba rashin sanin ƙalubalen ƙasar ba ce, illa rashin ƙarfin zuciya wajen aiwatar da hanyoyin magance su
- Ibrahim Abdulkarim ya kira matasa da su mallaki harkar siyasa tare da mara wa Obi baya, yana cewa goyon bayansa tamkar goyon bayan kansu ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja, Najeriya – Jigon jam'iyyar NDC, Ibrahim Abdulkarim, ya yi bayani kan bambancin burin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na APC, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar na ADC da Peter Obi gabanin zaɓen 2027.
Ibrahim Abdulkarim ya ce yayin da Tinubu da Atiku suka fi mayar da hankali kan neman ikon siyasa, Peter Obi kuwa yana neman damar yi wa ’yan Najeriya hidima da sauya fasalin ƙasar.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne ranar Talata, 1 ga watan Satumban 2026 yayin wata hira da shirin Politics Today na Channels Tv, inda ya tattauna halin da siyasar Najeriya ke ciki da kuma shirye-shiryen tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
An ce Obi na neman yi wa Najeriya hidima
A cewar Ibrahim Abdulkarim, babban bambanci tsakanin ’yan takarar ukun shi ne abin da ya sa kowannensu ke neman shugabancin ƙasar.
“Me ya bambanta su ukun? Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar suna neman mulki. Mista Peter Obi yana neman damar yi wa ƙasa hidima,” in ji shi.
Ya ce Obi na son ya ba da kansa domin sauya abubuwan da matasan Najeriya ke ganin sun gaza iya sauyawa da kansu.
“Yana son ya zo ya sadaukar da kansa domin sauya abin da muke ganin matasa ba za su iya yi wa kansu ba. Wannan shi ne abin da ya bambanta,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND
Ya ce ‘yan siyasa sun san matsalolin Najeriya
Jigon NDC ya ce babbar matsalar Najeriya ba wai rashin fahimtar matsalolin da ƙasar ke fuskanta ba ce.
A cewarsa, rashin ƙarfin zuciya da kuma niyya wajen aiwatar da hanyoyin magance matsalolin ne babban ƙalubalen.
Ibrahim Abdulkarim ya ce ’yan siyasa da dama, masana da masu tasiri a ƙasar sun san matsalolin Najeriya, kuma suna da masaniya kan matakan da ya kamata a ɗauka domin magance su.
“Yawancin manyan mutane a wannan ƙasa sun san matsalar, sun san abin da ke damunmu. Suna da mafita,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗannan mutane kan san abin da ya kamata a yi, amma ba sa iya faɗa ko kuma ba su da ƙarfin aiwatar da shi.
“Wasu za su ce maka, ‘Tabbas, ba zan iya faɗa ba.’ Wasu kuma su ce, ‘Ba zan iya ba, ba za mu iya yin hakan ba.’ Amma abin da muke ƙoƙarin yi shi ne mun ga wani mutum da yake da ƙarfin zuciya kuma yana son yin hakan,” in ji shi.
Ya ce matasa na goyon bayan Obi
Ibrahim Abdulkarim ya ce hakan ne ya sa shi da wasu matasan Najeriya suke mara wa Peter Obi baya a takarar shugaban ƙasa.
Ya ce goyon bayan Obi ba wai kawai tallafa wa mutum ɗaya ba ne, illa ƙoƙarin tabbatar da irin Najeriya da ’yan ƙasar ke son samu.

Source: Facebook
Peter Obi ya kalubalanci Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi ya kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya fito gaban ‘yan Najeriya kai tsaye.
Peter Obi ya bukaci Shugaba Tinubu da kada ya dogara da wakilai ko ‘yan siyasa wajen neman ƙuri’un jama’a.
Asali: Legit.ng

