An Gano Dan Siyasar da Ya Zai Zama Barazana ga Sabon Yunkurin Hadakar 'Yan Adawa
- Bolaji Abdullahi ya ce matsayar Peter Obi kan dawo da tallafin mai na iya zama barazana ga shirin haɗa kan jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027
- Ya ce ADC na ganin dawo da tallafin mai ba abin tattaunawa ba ne, yayin da jam’iyyar ta ce tana nazarin alkaluman tattalin arziki domin tabbatar da matsayarta.
- Abdullahi ya bayyana cewa rashin halartar Atiku Abubakar taron G100 ya faru ne saboda taron ya fi mayar da hankali kan haɗin gwiwar jam’iyyu, ba ’yan takarar shugaban ƙasa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja, Najeriya – Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya yi magana kan yunkurin hadakar 'yan adawa.
Bolaji Abdullahi ya ce matsayar Peter Obi kan batun tallafin mai na iya kawo cikas ga shirin haɗin kan jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki alkawarin da zai faranta wa ɗaliban Najeriya rai kan kuɗin NELFUND

Source: Facebook
Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 1 ga watan Agustan 2026 yayin wata hira da shirin Daybreak na Arise TV, inda yake bayanin dalilin da ya sa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, bai halarci taron G100 da aka gudanar a Abuja ba..
Saɓani kan batun tallafin mai
Bolaji Abdullahi ya ce rashin daidaituwar ra’ayi kan manufofin tallafin mai na iya raunana tubalin da aka kafa sabon shirin haɗin kan jam’iyyun adawa a kai.
“Wannan wani abu ne da masu shirya wannan haɗin gwiwa za su buƙaci su warware. Idan Peter Obi bai yarda da dawo da tallafin mai ba, alhali mu mun yarda, to me zai zama tushen haɗin kanmu?” In ji shi
Ya ƙara da cewa ADC a shirye take ta yi aiki tare da duk wata jam’iyyar da ta goyi bayan matsayinta kan batun tallafin mai.
Bolaji Abdullahi ya ce batun ba abin da za a yi sulhu a kansa ba ne ga ADC, yana mai cewa masana tattalin arziƙin jam’iyyar suna nazarin alkaluman sosai.

Kara karanta wannan
"Na san komai," Tsohon gwamna ya 'tsoratar' da yan Najeriya kan shirin dawo da tallafin fetur
“A wurinmu, wannan ba abin tattaunawa ba ne. Masanan tattalin arziƙinmu suna nazarin alkaluman dalla-dalla, kuma mun gamsu cewa wannan hanya ce da ya kamata mu bi,” in ji shi.
ADC na da yakinin za ta iya kayar da Tinubu
Bolaji Abdullahi ya ce ADC tana matuƙar goyon bayan shirin haɗin kan G100, amma hakan ba yana nufin jam’iyyar ba za ta iya kayar da jam’iyyar mai mulki ita kaɗai ba.
Ya ce haɗin kan jam’iyyun adawa zai ƙara musu damar samun nasara, amma ADC ba ta ɗora shirin haɗin gwiwar kan tilas ɗin samar da ɗan takara guda ɗaya ba.
“Mun yi amanna za mu iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a 2027 da kanmu. Idan muka samu damar cimma wannan haɗin gwiwa, hakan zai sauƙaƙa aikin ne kawai,” in ji Abdullahi.
Dalilin rashin halartar Atiku taron G100
Da yake magana kan rashin halartar Atiku Abubakar taron G100, Abdullahi ya ce taron ya fi mayar da hankali ne kan tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasa, ba ’yan takarar shugaban ƙasa ba.
Ya ce manufar taron ita ce duba hanyoyin da jam’iyyun adawa za su iya yin haɗin gwiwa da juna domin cimma burinsu na siyasa.
“Yadda muka fahimci taron, ya fi kasancewa tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasa fiye da tsakanin ’yan takara. Batun shi ne duba damar da ake da ita ta haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun siyasa,” in ji shi.

Source: Facebook
Atiku ya yi wa 'yan Najeriya alkawari
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi alkawari kan kananan hukumomi.
Atiku ya yi alkawarin tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomin Najeriya suna isa gare su kai tsaye idan ya lashe zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
