Kamfen Ya Fara Daukar Zafi, Peter Obi Ya Sake Kalubalantar Tinubu

Kamfen Ya Fara Daukar Zafi, Peter Obi Ya Sake Kalubalantar Tinubu

  • Peter Obi ya bukaci Shugaba Tinubu ya fito ya gana da ‘yan Najeriya kai tsaye maimakon dogaro da masu wakiltarsa wajen neman ƙuri’u
  • Obi ya ce shugaban da ke neman wa’adin mulki na biyu ya kamata ya bayyana nasarorin gwamnatinsa tare da amsa tambayoyin jama’a
  • Dan takarar NDC ya ce zaɓen 2027 ya kamata ya kasance gasar ƙwarewa, tarihi, manufofi da halayen ‘yan takara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Yayin da kamfen ɗin babban zaɓen 2027 ya fara ɗaukar sabon salo, ɗan takarar shugaban ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya fito gaban ‘yan Najeriya kai tsaye.

Peter Obi ya bukaci Tinubu, wanda shi ne ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, da kada ya dogara da wakilai ko ‘yan siyasa wajen neman ƙuri’un jama’a.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi babban rashi, tsohon alkalin Kotun Koli Umaru Kalgo ya rasu

Peter Obi ya kalubalanci Tinubu
Peter Obi yayin bude yakin neman zabensa Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya soki kamfen ta hanyar wakilai

A cikin wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar, Obi ya ce babu abin da ya kamata a kira “kamfen ta hanyar wakili” a zaɓen shugaban ƙasa, cewar rahoton jaridar Leadership.

Tsohon gwamnan na Anambra ya ce akwai alamun cewa Tinubu na shirin zama a Fadar Shugaban Ƙasa yayin da wasu ‘yan siyasa da aka ɗora wa aikin kamfen za su rika zuwa wajen jama’a a madadinsa.

Ya ce irin wannan tsari bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba kuma ya kamata ‘yan Najeriya su ƙi amincewa da shi.

Obi ya ce Tinubu na iya amfani da wakilai wajen wasu ayyukan gwamnati, amma bai kamata ya tura wani mutum ya gana da ‘yan Najeriya a madadinsa yayin da yake neman wa’adin mulki na biyu ba.

“Ya fito ya kare ayyukansa"

Obi ya ce zaɓen 2027 ba wani biki ba ne da wakilai za su gudanar a madadin ‘yan takara, domin ana neman wanda zai jagoranci sama da mutane miliyan 200, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

APM ta hutar da 'yan adawa, ta gano dan takarar da zai lallasa Tinubu a zaben 2027

Ya ce duk wanda ke neman shugabancin ƙasar dole ne ya kasance a shirye ya tsaya gaban jama’a, ya amsa tambayoyinsu tare da kare tarihin aikinsa.

“Ya kamata ‘yan Najeriya su ga ɗan takarar. Su ji ɗan takarar. Su yi wa ɗan takarar tambayoyi,” in ji Obi.

Ya ƙara da cewa hakan ya shafi dukkan manyan tarukan ƙasa, ciki har da taron Nigerian Bar Association (NBA), inda ake buƙatar ‘yan takarar shugaban ƙasa su bayyana matsayinsu kan halin da ƙasar ke ciki.

Ya ambaci taron zaman lafiya

Obi ya kuma soki rashin halartar Tinubu a taron yarjejeniyar zaman lafiya ta ƙasa da National Peace Committee ta shirya ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙasa Janar Abdulsalami Abubakar.

Ya ce rashin halartar shugaban ya nuna rashin girmama ƙoƙarin da Abdulsalami Abubakar, Bishop Matthew Hassan Kukah da sauran masu ruwa da tsaki ke yi wajen tabbatar da zaɓe cikin lumana.

Ya bukaci Tinubu ya yi wa jama’a bayani

Obi ya ce shugaban ƙasa da ke neman ƙarin shekaru huɗu ba zai iya ɓoye kansa a bayan ministoci, shugabannin jam’iyya, masu magana da yawunsa, gwamnoni ko wasu ‘yan siyasa ba.

Kara karanta wannan

APC: 'Dalilin Atiku na yin alkawarin dawo da tallafin man fetur idan an zaɓe shi'

Ya ce idan Tinubu ya yi imanin cewa gwamnatinsa ta yi nasara, ya kamata ya fito ya bayyana hakan da kansa ga ‘yan Najeriya.

Ya bukaci shugaban ya yi bayanin yadda tattalin arzikin ƙasar yake, matsin rayuwar da iyalai ke fuskanta da manufofin gwamnatinsa.

Haka kuma, ya ce ya kamata Tinubu ya bayyana wa jama’a abin da ya sauya tun shekarar 2023 da kuma abubuwan da zai yi daban idan aka sake zaɓarsa.

Peter Obi ya kalubalanci Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Peter Obi ba zai dawo da tallafin fetur ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa ta NDC, ya jaddada goyon bayansa ga cire tallafin man fetur a Najeriya.

Peter Obi ya ce zai kawo tsari mai kyau da zai karkatar da kudaden tallafin man da aka cire zuwa bangaren da yan Najeriya musamman talakawa za su amfana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng