Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yadda Arewa Ta Fi Cin Ribar Gwamnatinsa

Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Yadda Arewa Ta Fi Cin Ribar Gwamnatinsa

  • Ƙungiyar ACF da MBF sun soki ikirarin Shugaba Bola Tinubu cewa Arewacin Najeriya ce ta fi kowace ɓangare cin gajiyar sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa
  • Yayin da ACF da MBF suka bayyana ikirarin a matsayin abin mamaki da kuma na siyasa, Kiristocin Arewa sun yi sabanin haka, inda suka ce Tinubu ya yi kokari
  • Tinubu da APC sun dage cewa cire tallafin man fetur wani mataki ne mai wahala amma ya zama dole, wanda ya karkatar da kuɗi gwamnati zuwa wasu ɓangarori

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Ƙungiyoyin ACF da MBF sun yi watsi da ikirarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu cewa Arewacin Najeriya ce ta fi cin gajiyar sauye-sauyen tattalin arziƙin gwamnatinsa.

Ƙungiyoyin sun bayyana cewa matsalolin talauci da tsadar rayuwa da ke addabar Arewa sun sa ikirarin shugaban ya zama abin tambaya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya barke da murna bayan Najeriya ta samu wani cigaba

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya na bayani a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa Kiristocin Arewa sun saba da ACF da MBF, inda suka ce gwamnatin Tinubu na yin abin da ya fi na tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari.

Bayanin da Tinubu ya yi

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gaji matsalolin tallafin man fetur, tsarin musayar kuɗi, ƙarancin kuɗin shiga, ƙarancin dalar Amurka, hauhawar biyan basussuka da kuma ƙarancin zuba jari a muhimman ababen more rayuwa.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron tattaunawa kan manufofin APC domin bayyana nasarorin da shugaba Bola Tinubu ya samu a shekara 3..

Bayan sauye sauye, ya ce cinikayyar kayayyakin Najeriya ya inganta daga rarar Naira biliyan 44.8 daga 2023 zuwa kusan Naira tiriliyan 7.54 a cikin watanni uku na farko na 2026.

Shugaban ya ce GDP na ƙasar ya ƙaru da kashi 4.43 cikin 100 a zango na biyu na shekarar 2026, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa kusan kashi 15.4 cikin 100.

Kara karanta wannan

Nafiu Bala ya kawo sabon rikici a ADC kan yadda Atiku ke sukar Tinubu

Shugaban jam'iyyar APC a Najeriya
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Tinubu ya ce waɗannan nasarori na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ke son amfani da su wajen cimma burinta na mayar da tattalin arzikin Najeriya ya kai dala tiriliyan 1 nan da shekarar 2030.

Ya kuma jero ayyukan more rayuwa da suka haɗa da bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK), asusun lamunin ilimi na NELFUND da shirye-shiryen koyar da sana’o’i da fasaha.

Batun cire tallafin mai

Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda ya wakilci Tinubu a taron, ya ce cire tallafin man fetur wani mataki ne mai wahala amma wajibi domin sake karkatar da kuɗaɗen gwamnati zuwa wasu muhimman fannoni.

A cewar Yilwatda, tsohon tsarin tallafin man fetur ya kasance cike da almundahana da asara, yana cinye makudan kuɗin gwamnati da za a iya amfani da su wajen ilimi, tsaro, noma, lafiya da ababen more rayuwa.

Zargin APM kan Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APM ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya janye daga takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan tafiya hutu Turai 'Najeriya na ci da wuta'

Jam’iyyar ta yi zargin cewa matakin Tinubu na neman kotun Amurka ta hana FBI da DEA sakin wasu takardu da ake cewa suna da alaƙa da zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

APM ta ce abin da lauyoyin shugaban suke yi na ƙoƙarin dakile sakin takardun na iya sa ’yan Najeriya da sauran duniya su ɗauki matakin a matsayin wata alama ta amincewa da zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng